Mataimakin Gwamnan Kaduna ne dan takarar Sanata a APC
An bayyana Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Barnabas Bala Banted a matsayin wanda ya lashe zaben fid da gwani na takarar Majalisar Dattawa daga Kaduna ta Kudu a karkashin APC bayan ya kayar da abokin takararsa, Sanata Caleb Zagi. Zaben, wanda dubban wakilan jam’iyyar suka fito daga kananan hukumomi takwas na yankin don kada kuri’arsu, an […]
APC
An bayyana Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna, Barnabas Bala Banted a matsayin wanda ya lashe zaben fid da gwani na takarar Majalisar Dattawa daga Kaduna ta Kudu a karkashin APC bayan ya kayar da abokin takararsa, Sanata Caleb Zagi.
Zaben, wanda dubban wakilan jam’iyyar suka fito daga kananan hukumomi takwas na yankin don kada kuri’arsu, an gudanar da shi babu wata hatsaniya bayan sa rana ana dagewa har sau uku, abin da ya sa wadansu suka fara tababa kafin a karshe a gudanar da shi a filin wasa na garin Kafanchan.
A lokacin da yake bayyana sakamakon zaben, shugaban zaben, Mista Gabriel Isudari ya bayyana cewa Mataimakin Gwamnan ya lashe zaben ne da kuri’a 2,287 daga cikin kuri’a 2,558 da aka kada, inda abokin takararsa Caleb Zagi ya samu kuri’a 268.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan kammala zaben, Mataimakin Gwamnan wanda shi ne ya lashe zaben, ya yi alkawarin sauya irin kallon da ake yi wa yankin Kudancin Kaduna daga wurin tashe-tashen hankula zuwa cibiyar zaman lafiya ta hanyar samar da tsaro da ayyukan ci gaba don bunkasa harkokin tattalin arzikin yankin.
Tun bayan komawar Najeriya turbar dimokradiyya shekara 19 da suka gabata Jam’iyyar PDP ce ke wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa sai dai a yanzu da jam’iyyar APC mai mulkin jihar ta tsayar da Mataimakin Gwamnan, jama’a da dama za su zuba ido su ga ko a wannan karon za a samu sauyin jam’iyya ko a’a.