Mataimakin Gwamnan Kaduna ya fadi a Karamar Hukumar Kaura

Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna kuma dan takarar Sanata karkashin jam’iyyar APC, Barnabas Bala Bantex ya sha mummunan kaye a hannun Sanatan Kudancin Kaduna na PDP, Dakta Danjuma Tella Laah a Karamar hukumar Kaura, inda dukkaninsu suka fito. Barnabas Bala Bantex na APC ya samu kuri’a 9,071 yayin da Sanata Danjuma Laah na jam’iyyar PDP ya […]

Mataimakin Gwamnan Kaduna ya fadi a Karamar Hukumar Kaura

Yusuf Bala Barnabas

Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna kuma dan takarar Sanata karkashin jam’iyyar APC, Barnabas Bala Bantex ya sha mummunan kaye a hannun Sanatan Kudancin Kaduna na PDP, Dakta Danjuma Tella Laah a Karamar hukumar Kaura, inda dukkaninsu suka fito.

Barnabas Bala Bantex na APC ya samu kuri’a 9,071 yayin da Sanata Danjuma Laah na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 29, 356 kamar yadda jami’in tattara kuri’u, Luka K. Maude ya bayyana yanzun nan a garin Kafanchan, cibiyar Kudancin Kaduna.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta