Mataimakin Gwamnan Kebbi ya shawarci ’yan jarida kan tsare gaskiya
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Suleiman Mohammed Argungu, ya shawarci manema labarai da ke aiki a jihar su kasance masu gaskiya wajen gudanar da ayukkansu.Tsohon Mataimakin Gwamnan ya yi kiran ne a ofishin Jam’iyyar APC da ke Birnin Kebbi a lokacin da suke zantawa da wakilinmu, inda ya ce bai kamata ’yan jarida su […]
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi Alhaji Suleiman Mohammed Argungu, ya shawarci manema labarai da ke aiki a jihar su kasance masu gaskiya wajen gudanar da ayukkansu.
Tsohon Mataimakin Gwamnan ya yi kiran ne a ofishin Jam’iyyar APC da ke Birnin Kebbi a lokacin da suke zantawa da wakilinmu, inda ya ce bai kamata ’yan jarida su yarda wasu mutane su yi amfani da su don biyan bukatarsu ta kashin kai, musamman a wannan lokaci da rikice-rikicen addini da kabilanci da siyasa suka dabaibaye kasar nan. Alhaji Suleiman Argungu ya ce, “Yana da kyau ku kasance masu fadar gaskiya komai dacinta yayin gudanar da ayyukanku, kasancewarku madogarar samun sahihan labarai ga al’umma.”
Ya kara da cewa, “Wannan aiki naku ba aiki ne na mutanen banza ko makayarta ba, kuma muna sane da irin gudunmawar da kuke ba kasa da kuma jam’iyyarmu ta APC domin samun ci gaba mai ma’ana, a gaskiya kuna ba da gagarumar gudunmawa wajen kara kawo zaman lafiya da ci gabanta.”
Ya shawarci ’yan jarida su rika sa ido sosai kan masu bata masu suna a aikin jarida domin biyan wata bukata tasu.