Mataimakin Gwamnan Oyo ya koma APC

Sai dai ya ce yana nan daram a kan kujerarsa

Mataimakin Gwamnan Oyo ya koma APC

Mataimakin Gwamnan Jihar Oyo, Rauf Olaniyan, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Ya sanar da hakan ne ranar Lahadi, lokacin da yake zanta wa da manema labarai a ofishinsa da ke Ibadan.

Sai dai Rauf ya ce sauya shekar tasa ba ta shafi matsayinsa na Mataimakin Gwamna ba, inda ya ce har yanzu yana kan mukaminsa.

Ya ce ya dauki matakin ne bayan doguwar tattaunawa da magoya bayansa a fadin Jihar.

Mataimakin Gwamnan ya ce kowa na da ’yancin shiga ko fita daga dukkan jam’iyyar da ya ga dama, inda ya ce ilahirin magoya bayan nasa sun amince ya shiga APC.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa sauya shekar ta dada ta’azzara jita-jitar da ake yi a Jihar kan tsamin dangantaka tsakaninsa da Gwamna Seyi Makinde. (NAN)