Mataimakin Gwamnan Sakkwato ya yi murabus

Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Ahmed Aliyu, ya yi murabus daga mukaminsa ba tare da ya bayyana dalilinsa ba. Ahmed dai shi ne dan takarar Gwamnan Jihar a Jam’iyyar APC wanda hakan zai iya sa ya yi takara da tsohon maigidansa Aminu Waziri Tambuwal wanda ke neman takara a jam’iyyar PDP. Wata majiya ta kusa […]

Mataimakin Gwamnan Sakkwato ya yi murabus

Mataimakin Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Ahmed Aliyu, ya yi murabus daga mukaminsa ba tare da ya bayyana dalilinsa ba.

Ahmed dai shi ne dan takarar Gwamnan Jihar a Jam’iyyar APC wanda hakan zai iya sa ya yi takara da tsohon maigidansa Aminu Waziri Tambuwal wanda ke neman takara a jam’iyyar PDP.
Wata majiya ta kusa da Gwamna Tambuwal ta bayyana cewa ya ajiye mukamin nasa ne ba tare da an tilasta masa ba. Amma kuma wata majiyar ta bayyana cewa ya yi hakan ne bayan ya gano wata makarkashiya da ake shirya masa na tsige shi.
Majiyarmu ta gano cewa, Ahmed ya yi murabus ne ba tare da wani dalili ba, ya kuma mika wa majalisar dokokin jihar takardar murabus dinsa. Sai dai ba a karanta takardar murabus din ba a zauren majalisar.