Mataimakin kakakin APC na kasa ya fice daga jam’iyyar

Majiyoyi sun ce tsohon mataimakin kakakin na APC na ganawa da wata jam’iyya don samun tikitin takarar Gwamnan Kogi a zaben watan Nuwamba

Mataimakin kakakin APC na kasa ya fice daga jam’iyyar

Mataimakin Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar APC kuma mamba a Kwamitin Amintattu (NWC) na jam’iyyar, Hon. Muritala Yakubu Ajaka, ya ajiye mukaminsa tare da ficewa daga jam’iyyar nan take.

Wasu majiyoyi dai sun ce Hon. Ajaka na tattaunawa da wata jam’iyya da yake fata samun tikitin takarar Gwamnan Jihar  Kogi a zaben da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba.

Amma a wasikar ajiye aiki da ya aike wa Shugaban APC na Kasa, Abdullahi Adamu, Hon. Muritala, wanda jam’iyyar ta hana shi tsayawa takarar gwamnan jihar, ya ce ya fice daga ne saboda dalilai na kashin kansa.

“Na riga na sanar a hukumance ga shugaban jam’iyyar na mazabata ta Ajaka da ke Karamar Hukumar IgalaMela/Odu ta Jihar Kogi,” in ji shi.

A cewarsa, hadin kai da iya kamun ludayin jam’iyyar ya taimaka mata wajen samun nasara a zaben shugaban kasa da aka kammala, haka kuma kwarewan shugabancin jam’iyyar a matakin kasa zai taimaka wa gwamnati mai jiran gado.

Idan ba a manta ba, a baya Muritala ya kai koke ga kwamitin amintattun jam’iyyar kan hana shi tsayawa takarar gwamnan kogi Kogi a jam’iyyar, amma bai samu biyan bukata ba.

Wasu majiyoyi dai sun ce Hon. Ajaka na tattaunawa da wata jam’iyya da yake fata tsayawa takara a zaben gwamann jihar da ke tafe ranar 11 ga watan Nuwamba.