Mataimakin Shugaban AFMAN na kasa ya janye murabus din da ya yi

A ranar Litinin da ta gabata ne Mataimakin Shugaban kungiyar Arewa Film Makers Association of Nigeria (AFMAN) na kasa Malam Salisu Muhammad Ofisa ya janye murabus din da ya yi.Ya ce, a lokacin ba kawai daga mukaminsa na mataimakin shugaban kungiyar na kasa ya sauka ba, a’a, ya ma fice daga kungiyar.  Ya ce: “Na […]

Mataimakin Shugaban AFMAN na kasa ya janye murabus din da ya yi

A ranar Litinin da ta gabata ne Mataimakin Shugaban kungiyar Arewa Film Makers Association of Nigeria (AFMAN) na kasa Malam Salisu Muhammad Ofisa ya janye murabus din da ya yi.
Ya ce, a lokacin ba kawai daga mukaminsa na mataimakin shugaban kungiyar na kasa ya sauka ba, a’a, ya ma fice daga kungiyar.  
Ya ce: “Na yi murabus ne sakamakon matsalolin cikin gida, inda maganganun suka rika tasowa a gefe ba tare da an same ni ba, sai na ga idan har na yi wani abu da ba daidai ba kamata ya yi a zauna da ni, a fada mini.”
Ya ce ya koma kan mukaminsa ne bayan an gano bakin zaren matsalolin sakamakon zaman da kungiyar ta yi.
Da wakilinmu ya tambaye shi an ce babban makasudin yin murabus dinsa ya shafi batun tafiyar ‘yan fim kwas Indiya ne, sai ya ce, “ba shi ba ne, kodayake wata-kila wannan dalilinma na daya daga ciki. Rigimar cikin gida ce, tun da an sasanta babu batun tone-tone kuma.” Inji shi.
Sakataren kungiyar Arewa na kasa Salisu Sule Katsina ya ce a ko’ina akan samu matsalolin cikin gida, “hakan ce ta faru a Arewa, sai muka ga bai kamata ya yi murabus ba, idan aka yi la’akari da irin gudunmuwar da yake bayarwa. Mun nuna masa muhimmancinsa a Arewa, muka ce masa koda babu abin da aka yi masa ya ce zai yi murabus don radin kansa ba za mu bar shi ba.” Inji Salisu.
Shugaban Arewa reshen Jihar Kano Isma’il Afakallah ya ce ko harshe da hakori sukan saba, inda bayan an gano bakin zaren ne ya sanya kungiyar ta kara dunkulewa wurin daya.
A cikin wadanda suka halarci zaman akwai Ibrahim Mandawari da Hamisu Lamido Iyantama da Ishak Sidi Ishak da Isma’il Naabba Afakallah da Bawa M Ahmad da Umar Kanu da Salisu Sule Katsina.