Mataimakin Shugaban kasa ya bude ayyuka a Jihar Bauchi

Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Muhammad Namadi Sambo ya kaddamar da ayyuka da dama a yayin ziyarar yini biyu da ya kai Jihar Bauchi, inda a ranar Asabar ya bude ofishin ma’aikatar kasa da Safiyo ta jihar da aka samar mata da kayan aiki na zamani domin adana bayanai da inganta fasalin rabon filaye a jihar. […]

Mataimakin Shugaban kasa ya bude ayyuka a Jihar Bauchi
Mataimakin Shugaban kasa ya bude ayyuka a Jihar Bauchi

Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Muhammad Namadi Sambo ya kaddamar da ayyuka da dama a yayin ziyarar yini biyu da ya kai Jihar Bauchi, inda a ranar Asabar ya bude ofishin ma’aikatar kasa da Safiyo ta jihar da aka samar mata da kayan aiki na zamani domin adana bayanai da inganta fasalin rabon filaye a jihar. Daga nan ya wuce unguwar masana’antu inda ya bude kamfanin taki na jihar da gwamnati ta sake yi masa gyare-gyare.

Alhaji Namadi Sambo ya kaddamar da makarantar almajiran allo (Tsangaya) a garin Buzaye da ke karamar Hukumar Bauchi kafin ya wuce zuwa sabon filin jirgin saman Bauchi da aka kammala aikinsa da gandun daji na Yankari inda ya bude wasu gine-gine da aka gina don inganta dajin.
A jawabin Alhaji Namadi Sambo ya ce an gina makarantun Tsangaya 120 a Arewa, kuma an kaddamar da ta farko a Jihar Sakkwato da Jigawa yanzu kuma an kaddamar da uku a Buzaye da Sade da Azare a Jihar Bauchi. Ya ce dalibai za su rika kwana a makarantun da aka mayar da su karkashin gwamnatin jihar domin lura da su tare da samar da duk kayan aikin da suka dace don koyar da ilimin addini da na zamani.
Alhaji Namadi Sambo ya kuma bude Jami’ar Jihar Bauchi a garin Gadau inda ya yaba wa kokarin gwamnatin Malam Isa Yuguda wajen bunkasa ilimi a jihar, ya ce gwamnatinsu karkashin Shugaba Jonathan ta himmatu wajen ba da fifiko ga fannin ilimi.
Gwamna Isa Yuguda ya yaba da ziyarar Mataimakin Shugaban kasar a jihar, inda ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da ba gwamnati goyon baya don gudanar da ayyukan inganta rayuwar jama’a. Gwamna Yuguda ya yaba wa tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu kan tsara Jami’ar Jihar shi kuma ya aiwatar da ita har aka bude ta.