Mataimakin shugaban kasar Malawi ya mutu a hatsarin jirgin sama

Duk mutanen da ke cikin jirgin saman sun rasu a sakamakon hatsarin.

Mataimakin shugaban kasar Malawi ya mutu a hatsarin jirgin sama

Gwamnatin kasar Malawi ta sanar da rasuwar mataimakin shugaban kasar, Saulos Chilima a hatsarin jirgin sama.

Shugaban kasar, Lazarus Chikwera ya sanar a safiyar Talata cewa hatsarin jirgin da Mista Chilima ke ciki ya yi ajalin duk wadanda ke ciki.

Shuagaba Chikwera ya ce, “jirgin ya yi karo ne da wani dutse, lamarin da ya yi sanadin tarwatsewarsa da mutanen ciki.”

Tun a ranar Litinin hukumomin kasar suka sanar da bacewar jirgin sojojin da ya dauko matakin shugaban kasar, inda nan take aka shiga lalube gano shi.

Masu aikin ceto sun tsinci gano karkacen jirgin da da wani a kasar .

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Crypto Zai Haɓaka Tattalin Arzikin Najeriya

NLC ta yi watsi da ƙara kuɗin kiran waya da data

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji