Mataimakin Shugaban Kenya ya isa Kotun Hague
A ranar Talatar da ta gabata ne Mataimakin Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya isa birnin Hague domin ci gaba da fuskantar shari’a a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya wato ICC.Ana zargin Mista Ruto ne da laifin kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa na shekarara 2007. Fiye da mutane dubu […]
A ranar Talatar da ta gabata ne Mataimakin Shugaban kasar Kenya, William Ruto ya isa birnin Hague domin ci gaba da fuskantar shari’a a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya wato ICC.
Ana zargin Mista Ruto ne da laifin kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasa na shekarara 2007. Fiye da mutane dubu daya ne suka rasa rayukan su a tarzomar.
A watan Disambar shekarar 2014 ne aka janye karar da ake tuhumar Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, wanda aka tuhumarsu tare. Masu gabatar da karar sun shigar da takardar bukatar janye tuhumar bayan da alkalan kotun suka ki ba su wani karin lokaci na tattara bayanai. Ofisihin masu gabatar da karar ya ce gwamnatin kasar ta ki ta mika cikakkun shaidu.
Kodayake, kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Human Right Watch ta ce, matakin wani koma baya ne ga yunkurin da ake na kawo karshen cin zarafin jama’a a kasar.
Mista Ruto ya samu rakiyar ’yan majalisa 40 zuwa Filin Jirgin Saman Jomo Kenyatta da ke birnin Nairobi.