Mataimakin Shugaban Majalisar Taraba ya tsallake harin makasa

Kimanin mako daya da mutuwar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Taraba Mista Haruna Tsokwa, wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari ga mataimakinsa Tanko Maikarfi a lokacin da ya kai ziyara ga wani abokinsa a Jalingo fadar jihar. ’Yan bindigar sun bi shi gidan abokinsa da ke Unguwar […]

Mataimakin Shugaban Majalisar Taraba ya tsallake harin makasa
Mataimakin Shugaban Majalisar Taraba ya tsallake harin makasa

Kimanin mako daya da mutuwar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Taraba Mista Haruna Tsokwa, wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari ga mataimakinsa Tanko Maikarfi a lokacin da ya kai ziyara ga wani abokinsa a Jalingo fadar jihar.

’Yan bindigar sun bi shi gidan abokinsa da ke Unguwar Malam Joda ne da ke Jalingo a ranar Asabar da ta gabata da misalin karfe 7:40 minti 10 bayan ya bar gidan.
Abokin Alhaji Salihu Yusuf Sansani ya ce, kimanin minti goma bayan ya bar gidansa tare da Mataimakin Shugaban, makwabta sun kira shi a waya cewa wasu ’yan bindiga sun kai hari gidansa. Ya ce ya yi saurin sanar da ’yan sanda, sai dai kafin su isa gidansa maharan sun yi gaba, amma sun iske matarsa cikin kaduwa.
Sansani ya ce ’yan bindigar su biyar sun rufe fuskokinsu, kuma sun tura matarsa zuwa dakin karbar baki inda suka fara cewa, “ina Mataim akin Shugaban Majalisar? Ina Mataimakin Shugaban Majalisar?” Ya ce sun daure hannunwan matarsa tare da toshe bakinta da tsumma don kada ta yi ihu. Kuma sun bincika gidan kaf da sunan gano wani fayil da suka ce Mataimakin Shugaban Majalisar ya boye a nan, inda suka yi ta tambayar matarsa “inda fayil din da Mataimakin Shugaban Majalisar ya boye a nan gidan yake,” ita kuma ta shaida musu cewa ba ta san komai game da fayil din ba.
Sansani ya ce ’yan bindigar sun bar gidan tare da alkawarin dawowa don bincikar Mataimakin Shugaban da suka ce kusan kullum yana gidan domin yin taro.
Da aka tuntubi Maikarfi ya ce, “Na kadu da na ji wasu ’yan bindiga na neman rayuwata kwanakin kadan da muka rasa shugaban majalisa, ban san su wane ne ba, amma hakika Allah zai fallasa su. Ban damu ba in suka kashe ni saboda tsayawuta a kan gaskiya, domin na san akwai ranar da Allah zai yi mana hisabi.”’
Ya ce ya kai rahoton lamarin ga Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Jubril Adeniji. Kuma Kakakin ’Yan sandan Jihar Joseph Kwaji ya tabbatar da samun rahoton Mataimakin Shugaban, inda ya ce sun fara binciken lamarin.
Marigayi Shugaban Majalisar ya taba tsallake harin ’yan bindiga a hanyar Akwanga zuwa Abuja a watan Satumban bara, amma odilansa ya rasa ransa, wani kuma ya samu raunin harbin bindiga a harin.