Mataimakin shugaban Miyetti Allah ya ɓata

Ƙungiyar makiyaya ta Miyetta Allah (MACBAN) ta  ce mataimakin shugabanta na ƙasa, Injiniya Munnir Atiku Lamiɗo ya ɓata. Kakakin MACBAN na ƙasa, Alhaji Muhammad Nura Abdullahi ne ya sanar da hakan ranar Juma’ar nan. Ya ce “ya bar gidansa dake jihar Katsina ranar Juma’a 23 ga Yuni 2023 da nufin tafiya Kaduna. Miyetti Allah ta […]

Mataimakin shugaban Miyetti Allah ya ɓata

Ƙungiyar makiyaya ta Miyetta Allah (MACBAN) ta  ce mataimakin shugabanta na ƙasa, Injiniya Munnir Atiku Lamiɗo ya ɓata.

Kakakin MACBAN na ƙasa, Alhaji Muhammad Nura Abdullahi ne ya sanar da hakan ranar Juma’ar nan.

Ya ce “ya bar gidansa dake jihar Katsina ranar Juma’a 23 ga Yuni 2023 da nufin tafiya Kaduna.

Miyetti Allah ta yi tir da Gwamnatin Tarayya kan kisan makiyaya a Nasarawa

Miyetti Allah za ta iya kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga – Sarkin Musulmi 

“A ranar Alhamis an gano motarsa a tsakanin Jos da Kaduna kusa da Mararrabar Jos kuma duk wayoyinsa na salula na ciki.

“Sai dai duk matakan da aka ɗauka na gano inda yake sun ci tura.”

Kakakin ƙungiyar ya buƙaci duk wanda ke da labarin inda mataimakin shugaban ya shiga ya sanar da ofishin ƴan sanda mafi kusa.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan