Mataimakin Shugaban PCNI Tijjani Tumsah ya ziyarci GGTC Dapchi

Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI) a karkashin jagorancin Janar T. Y. danjuma GCON (mai ritaya) ya jajanta wa Gwamnan Jihar Yobe, Dokta Ibrahim Geidam da Hakimin Dapchi, Alhaji Kachalla Yuroma. Janar danjuma. Mataimakin Shugaban Kwamitin PCNI Alhaji Tijjani Tumsah ne ya wakilci Janar danjuma, a yayin ziyarar jajantawar. A lokacin […]

Mataimakin Shugaban PCNI Tijjani Tumsah ya ziyarci GGTC Dapchi

Kwamitin Shugaban kasa kan Farfado da Arewa maso Gabas (PCNI) a karkashin jagorancin Janar T. Y. danjuma GCON (mai ritaya) ya jajanta wa Gwamnan Jihar Yobe, Dokta Ibrahim Geidam da Hakimin Dapchi, Alhaji Kachalla Yuroma. Janar danjuma. Mataimakin Shugaban Kwamitin PCNI Alhaji Tijjani Tumsah ne ya wakilci Janar danjuma, a yayin ziyarar jajantawar. A lokacin da suke garin Dapchi ya isar da sakon Shugaban cewa, “Wannan harin mai ban takaici ya auku ne a daidai lokacin da rundunar Operation Lafiya Dole ke shawo kan munanan hare-haren ta’addanci a Arewa maso Gabas, kuma harkokin rayuwar jama’a suka fara farfadowa a galibin garuruwa.”

Ya bai wa Hakimin da wakilan iyayen yaran tabbacin cewa Kwamitin PCNI zai yi aiki tare da daukacin masu ruwa-da-tsaki don tabbatar da ceto ’yan matan su dawo lafiya kalau.

Alhaji Tumsah daga baya ya kewaya Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta ’Yan mata ta Dapchi domin jin yadda aka keta harkar tsaronta. Ya bayar da tabbaci ga wakilan ’yan matan da aka sace cewa gwamnati za ta tura sojoji da dukan jami’an tsaro na farin kaya domin tabbatar da ganin an ceto ’yan matan sun dawo lafiya. Jagoran wakilan iyayen ’yan matan, Malam Bashir Manzo, ya ce wakilan za su ci gaba da bai wa Kwmaitin PCNI cikakkun bayanai kan yawan daliban, wadanda ba a kirga da su ba, tunda har yanzu iyaye na zuwa daga yankunan karkara. Kuma Tumsah ya yi karin haske kan bullo da tsarin tsaro ga makarantu, kuma manyan makarantun sankandare, wadanda suke da dalibai 2000 da ke halartar makarantu 43 a fadin kasar nan, za a fadada su domin dada daukar daliban da suke fuskantar hadari daga Arewa maso Gabas. daliban aji daya na babbar sakandare za a sake bin kadin lamarinsu tare da masu ruwa-da-tsaki don fito da ingantaccen tsarin da za a ba su kariya daga hare-hare, sannan a tabbatar da cewa sun ci gaba da da neman ilimi a karkashin tsarin kariya da nagartarsa ta yi daidai da yadda lamarin yake a sauran sassan duniya.