Mataimakin shugabancin PDP: Matasan Arewa maso Gabas suna bayan Manji

Majalisar matasan Najeriya (CANYF). karkashin ‘ya’yan Jam’iyyar PDP na yankin Arewa mso Gabas sun nuna goyon bayansu ga Alhaji Musa Usman Manji a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar. Majalisar matasan sun ce sun dauki wannan matakin ne na tsayawa a bayan Manji domin ya wakilci matasan Najeriya a cikin sauran ‘yan takara, sannan kuma sun yi […]

Mataimakin shugabancin PDP: Matasan Arewa maso Gabas suna bayan Manji

Majalisar matasan Najeriya (CANYF). karkashin ‘ya’yan Jam’iyyar PDP na yankin Arewa mso Gabas sun nuna goyon bayansu ga Alhaji Musa Usman Manji a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar.

Majalisar matasan sun ce sun dauki wannan matakin ne na tsayawa a bayan Manji domin ya wakilci matasan Najeriya a cikin sauran ‘yan takara, sannan kuma sun yi hakan ne domin cigaban Najeriya musamman matasa.

A jawabin kungiyar ta CANYF, wanda shugabanta na kasa Dokta Marwanu Aji Muhammad da sakataenta Mista Yunana Joseph Aboki suka sanya wa hannu, sun ce suna kokari ne domin ganin cewa sun kara karfafa jam’iyyar bayan kayan da ta sha a zabukan da suka wuce, wanda hakan ya sa wasu da yawa daga cikin manyan jam’iyyar suka fice

Sannan suka yi kira ga sauran ‘yan takaran kujeran mataimakin shugaban jam’iyyar da ajiye aniyarsu ta takara, su bar wa Manji kujerar.

“Abin da ya sa muke so Manji ya zama mataimakin shugaban jam’iyyar shi ne yadda muka ga cewa shi shugaba ne mai mutunci, sannan kuma ya yi kokari kwarai da gaske wajen tabbatar da cewa jam’iyyar ta samu nasara. Nasara mai daurewa da jam’iyyarmu ta samu ya ta’allaka ne da mutuncinta da kuma yadda take kare akidun da asalin wadanda suka assasa jam’iyyar suka gindiya tun farko.

“Don haka ne muke ganin cewa jam’iyyarmu tana bukatar shugabanni masu mutunci, kuma matasa masu jinji a jika kuma suke da ilimi da tunani a kan yadda za su magance kura-kuren da aka tafka a baya. Alhaji Manji mutum ne mai akidar jam’iyya, wanda ya san mutuncin mutane, kuma ya san abin da ke damunsu, kuma ya san ya kamata. Kuma ya zama dole ga jam’iyyar ta tabbatar da cewa an samu zaman lafiya da cigaban kasarmu, da hadin kan ‘yan siyasa,” inji su.