Mataimakin Sufeto Janar ya nemii hadin kan sarakunan Jihar Edo
Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan sandan Najeriya, mai kula da Jihohin Edo Delta da Bayelsa Musa Daura, ya bukaci sarakunan gargajiyar wadannan jihohin da su bai wa Hukumarsa hadin kai, don samun nasarar tunkarar masu aikata miyagun laifuka a jihohin. Babban jami’in ’yan sandan ya gabatatar da wannan bukatar ne a yayin da ya yi […]
Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan sandan Najeriya, mai kula da Jihohin Edo Delta da Bayelsa Musa Daura, ya bukaci sarakunan gargajiyar wadannan jihohin da su bai wa Hukumarsa hadin kai, don samun nasarar tunkarar masu aikata miyagun laifuka a jihohin.
Babban jami’in ’yan sandan ya gabatatar da wannan bukatar ne a yayin da ya yi kira na musamman ga Otaru na Auchi Alhaji H.A.Momoh a lokacin da ya kai ziyararsa ta farko a yankin Arewacin jihar. Daura wanda ya bayyana cewa rashin samun goyon baya daga sarakuna da sauran mutane yana janyo wa jami’an tsaro da kuma aikin tsaron kansa cikas a ko’ina cikin kasar nan.
Ya ce ba za a iya ci ma nasara ba muddin ba a samun taimakon hadin kai daga Sarakunan gargajiya airin wannan halin da kasa take ciki, kuma sai ya yi bayanin cewa ba za a bar maganar tsaro a hannun ‘yan sanda su kadai ba, don haka taimakon da mutane za su bayar abin bukata ne ga aikin tsaron kasa, ta yadda za a bai wa al’umma damar runtse idanunsu a lokacin da suke barci.
Da yake tofa albarkacin bakinsa, Alhaji Momoh Ikelebe na uku, ya tunatar wa babban bakonsa da cewa akwai nauyin da ya rataya a wuyansa na jama’a a matsayinsa na Mataimakin Sufeto Janar (AIG), wajen ganin jihohi ukkun da yake kula da su. Don haka ya roki Allah ya ba shi nasara game da aikin tsaron da yake yi wa jama’a.
Alhaji Momoh ya ce mutanen Najeriya za su kasance a cikin zaman lafiya matukar kowa ya yi aikinsa da kyau, amma kuma ya nuna damuwarsa game da abin da ya yi nuni da cewa, ‘Ina ganin mutane da yawa a cikin ‘yan Najeriya ba su san Allah da hakika ba. Sannan sai ya karkare da cewa matsalar ita ce akwai mutane da dama suna so wa wasu ’yan uwansu abin da ba su so ya auku a kansu.”