Mataimakiyar Shugabar Mata ta APC a Yobe ta rasu
Za a yi jana’izarta a yau Lahadi da ƙarfe 4:00 na yamma a Masallacin Cibiyar Kula da Addinin Musulunci da ke Damaturu.
Mataimakiyar Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC a Jihar Yobe, Hajiya Fatima Mairiga (Gwamnati), ta rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Ta rasu ne a ranar Asabar a Kano, inda take karɓar magani, kamar yadda wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe, Hussaini Mai Suleh, ya fitar ta bayyana.
- Auren Gata: Gwamnatin Kano ta sanya ranar aurar da mutum 1,500
- Kyawawan ɗabi’un Arewa sun gushe — Ango Abdullahi
Sanarwar ta ce rasuwarta babban rashi ne ga Jam’iyyar APC da kuma al’ummar Jihar Yobe.
Marigayiyar ta kasance fitacciyar ’yar siyasa, inda ta taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan mata da ƙarfafa goyon bayan jam’iyyar APC a ƙananan hukumomi 17 na Jihar Yobe.
Za a yi jana’izarta a yau Lahadi da ƙarfe 4:00 na yamma a Masallacin Cibiyar Kula da Addinin Musulunci da ke Damaturu.
Rasuwarta ta jefa ’yan uwa, abokan siyasa da magoya bayanta cikin jimami, yayin da ake sa ran jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar za su halarci jana’izarta.