Matakan da ake dauka za su kawo karshen karancin man fetur – Ya’u babura

Wani dan kasuwa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum da ke Kano, Alhaji Sani Ya’u babura ya ce matsalar karancin man fetur ta kusa zuwa karshe saboda kyawawan matakai da ake dauka wajen wadata kasar nan da man fetur.Alhaji Sani babura ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a […]

Matakan da ake dauka za su kawo karshen karancin man fetur – Ya’u babura
Matakan da ake dauka za su kawo karshen karancin man fetur – Ya’u babura

Wani dan kasuwa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum da ke Kano, Alhaji Sani Ya’u babura ya ce matsalar karancin man fetur ta kusa zuwa karshe saboda kyawawan matakai da ake dauka wajen wadata kasar nan da man fetur.
Alhaji Sani babura ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Kano, inda ya ce abubuwa da yawa ne suka haifar da matsalar man fetur a Najeriya wadanda suka hada da canjin gwamnati da aka samu da yadda tsarin hulda da bankuna suka sauya da kuma yanayin karfin kasuwar albarkatun man fetur a kasuwar duniya.
dan kasuwar ya bayyana cewa manyan kamfanonin sayar da mai da masu harkar sayar da mai masu zaman kansu suna matukar kokari wajen ganin ba a shiga matsalar man fetur ba, amma yadda yanayi ya kasance ne ya sa ake fama da wahalar mai duk da cewa an fara daukar kwararan matakan ganin al’amura sun inganta ta fuskar samar da man fetur.
Alhaji Sani Ya’u babura ya ce babu wani mutum ko wasu mutane da suke haddasa matsalar mai da gangan, amma akwai yanayin da dole ne sai an dan samu matsala kafin komai ya inganta musamman idan aka samu canjin gwamnati a kowace kasa, don haka ya tabbatar wa al’ummar kasar nan cewa nan da ’yan kwanaki al’amura za su canja cikin yardar Allah.
Alhaji Sani ya ce yana da kyau Gwamnatin Tarayya ta yi kokarin inganta matatun man fetur da ake da su ta yadda za su iya samar da wani adadi na man da ake bukata a cikin kasa, inda ya ce kudinda ake kashewa wajen tace mai a kasashen waje suna da yawa. “Amma idan aka gyara matatun man da muke da su al’amura za su inganta kamar yadda ake gani a sauran kasashe masu arzikin mai.