Matakan da El-Rufa’i ya dauka kan makarantun firamare sun yi daidai – Farfesa Dadari

Aminiya: A matsayinka na masani kan harkokin ilimi me za ka ce kan korar dubban malaman makarantun firamare da ake shirin yi a Jihar Kaduna, saboda rashin cin jarrabawar da aka yi masu? Farfesa Dadari: Maganar gyara harkokin ilimi da Gwamna Nasiru El-Rufa’i yake yi a Jihar Kaduna, ya yi daidai. Domin Jihar Kaduna ce […]

Matakan da El-Rufa’i ya dauka kan makarantun firamare sun yi daidai – Farfesa Dadari

Aminiya: A matsayinka na masani kan harkokin ilimi me za ka ce kan korar dubban malaman makarantun firamare da ake shirin yi a Jihar Kaduna, saboda rashin cin jarrabawar da aka yi masu?

Farfesa Dadari: Maganar gyara harkokin ilimi da Gwamna Nasiru El-Rufa’i yake yi a Jihar Kaduna, ya yi daidai. Domin Jihar Kaduna ce cibiyar Arewa, kuma nan ne aka fara kafa jami’a, wato Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, jami’ar da tafi kowace shahara a Afirka ta Yamma. Saboda haka idan Gwamna El-Rufa’i ya ce zai gyara harkokin ilimi a Jihar Kaduna, addu’a ya kamata a yi masa. 

Wannan mataki da Gwamna El-Rufa’i ya dauka kan gyara harkokin ilimi, musamman bangaren makarantun firamare ya yi daidai a wajen masu son gaskiya da ci gaba. Amma a wajen wadanda ba sa son  gaskiya da cigaba bai yi daidai ba. Domin a baya, an gina makarantun firamare ne a kan tubar siyasa, an bi dukan kauyuka an gina makarantun firamare. Akwai kauyukan da ba su kamata a gina musu makarantun firamare ba, domin za ka ga wani kauyen bai kai nisan kilomita daya tsakaninsa da wani kauyen ba, amma an gina masa makarantar firamare. Za ka ga irin wadannan makarantu babu kujeru, za ka samu malamai sama da 20 a rubuce, amma ba sa zuwa aiki. Kuma yawaicin malaman ba sa son zuwa kauyuka, sun fi son su zauna a gari. Kuma yawaicin irin wadancan malamai, an dauke su aiki ne ta hanyar alfarma. Za ka ga manyan mutane sun kawo yaransu sun ce a dauke su aikin koyarwa a makarantun firamare, domin su ci abinci, ba tare da suna da ilimin koyarwar ba. Wadannan malamai ba sa sa ’ya’yansu a cikin makarantun da suke koyarwa, suna kai ’ya’yansu makarantun kudi ne.  

Wannan matsala ce ta kasar nanbaki daya, ba Jihar Kaduna kadai ba. Idan aka tantance malaman makarantun firamare na kasar nan, za a samu baragurbi da yawa. Don haka idan Gwamna El-Rufa’i ya ce zai yi gyara kan wannan al’amari bai yi laifi ba, a wajen wanda yake son ci gaba.  

Tsarin ilimi ya lalace, shi kuma Gwamna El-Rufa’i yana son ya yi gyara, don haka ya dauki wannan mataki. Idan aka dauki malaman nan kan ka’ida, sai su dauki aikin da muhimmanci. Amma a baya, an rika daukar malamai ba bisa ka’ida ba. Za ka ga wani bai iya rubuta sunansa, amma an dauke shi aiki a matsayin malamin da zai je ya koyar a makarantar firamare.Wannan abu da Gwamna El-Rufa’i yake yi daidai ne, domin duk wanda aka dauka bisa ka’ida zai rike aikin da muhimmanci ya zauna ya yi tsakaninsa da Allah.  Ba mu ce a kori mutane ba, amma bai kamata a dauki mutane aiki ya kasance ba sa yin aikin ba. 

Ya kamata malami ya zamanto mai ilimintar da kansa a kullum ta hanyar bincike da karantu da karanta jaridu da sauraron rediyo, domin ya san abubuwan da suke faruwa na yau da kullum. Amma yanzu a tambayi malami wane ne Shugaban Majalisar Dattawa ya ce bai sani ba, bai kamata ba.  

Jarrabawar da aka yi wa malaman nan a Jihar Kaduna, ya kamata a tantance wadansu a sake nazari. Wadanda ba su cancanta ba a sallame su, a dauko wadanda suke da takardar koyarwa.  

 Kuma a gyara wa malaman albashinsu idan ana son su yi aiki, a takaice a rika biyan karamin malami albashin Naira dubu 50 a wata. Kuma a tabbatar cewa duk malamin da aka tura wani kauye, ya tafi can. Kada a kara yarda malamai su rika bayar da cin hanci, suna kin tafiya kauyuka don su zauna a gari. 

Aminiya:  kwanakin baya gwamnatin Jihar Kaduna ta ce za ta dauki wasu tsangayoyi na jami’ar jihar, ta kai wasu yankuna na jihar yaya kake ganin wannan mataki?

Farfesa Dadari: Idan Gwamnan El-Rufa’i ya yi haka ya yi kuskure, domin ko a wajen taron masu ruwa-da-tsaki na Jihar Kaduna da aka yi a kwanakin baya, na fito na fada masa cewa babu yadda za a yi a kasa tsangayoyin jami’a kamar gyada. A duk duniya yin haka ba ya da wani tasiri a fannin ilimin jami’a. Ana cewa kasa ba ta da kudi, Jihar Kaduna ma ana cewa ba ta da kudi. Yanzu  ka sanya jami’a a garin  Kaduna  ka yi zirga-zirgar  daga Kaduna zuwa Lere don duba wata tsangaya ko ka tafi Birnin Gwari ko ka tafi Zangon Kataf don duba wata tsangaya nawa za ka kashe? Wadannan kudade da za a rika kashewa ba su isa a yi amfani da su a sayi wasu na’urori da za a sanya a wannan jami’a ba?

Babu shakka inda aka ajiye wannan yanzu ya yi kadan, ya kamata a samu wani babban fili kamar muraba’in mita dubu 5 ko dubu 10 a hanyar Birnin Gwari ko hanyar Kachiya  a shinfida wannan jami’a a ajiye ta wuri daya, wadda nan da shekara 100 ba za a yi kukan rashin fili, na gina wani abu ba. Kamar yadda aka gina Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya. Amma rarraba tsagayoyin jami’a ba ya da wani tasiri. 

Aminiya: Har ila yau a ’yan kwanakin nan gwamnatin Jihar Kaduna ta sake yunkurowa don rage yawan ma’aikatan kananan hukumomin jihar me za ka ce kan wannan lamari?

Farfesa Dadari: Maganar ma’aikatan kananan hukumomi kamar maganar malaman makarantun firamare ne, a baya an dauki mutane aiki a kananan hukumomi ba kai ba gindi. An dauki mutane ba sa aikin komai a kananan hukumomi an ce su je su ci abinci. Na san mutane da dama wadanda yaransu suna makaranta ne amma sunayensu suna wasu kananan hukumomi ana biyansu albashi a matsayin ma’aikata. Don haka yanzu a kananan hukumomi za ka ga babu kowa sai wata ya kare, mutane su je su karbi albashi.  Babu inda ake yin irin wannan sai a Najeriya, kuma babu yadda za a samu ci gaba a irin wannan tsari. Amma saboda mutane ba sa son gaskiya, sai tsine wa wannan yunkuri suke yi. Wannan abu da Gwamna El-Rufa’i yake yi yana yi ne domin ci gaban al’ummar Jihar Kaduna. Duk jihohin Najeriya irin abubuwan da suke faruwa ke nan.

Aminiya: Ganin ana ta koke-koke kan rashin ayyukan yi, ba ka ganin irin wadannan abubuwa za su kara kawo rashin aikin yi a Jihar Kaduna?

Farfesa Dadari: Akwai sana’o’i da dama da mutane za su iya shiga su koya. Ya kamata bayan mun sa yaranmu a makaranta mu rika sanya su a wuraren koyon sana’a. Ga sana’o’i nan daban-daban da za mu iya sanya yaranmu su koya. Sannan ga sana’ar noma wadda ta kunshi abubuwa da dama da za mu sa yaranmu su koya. Don haka ba dole ne sai mun yi aikin gwamnati ba. Kuma bai kamata don mutum yana aikin gwamnati ya ki yin wata sana’a ba, domin yanzu albashi ba zai ishi ma’aikaci ba.