Matakan kare kai daga yawan bacin rai

Fushi ko bacin rai na daya daga cikin wasu dabi’u da Allah subhanahu wata’ala ya halicci dan Adam da su. Shakka babu muddin dan Adam yana raye a wannan duniya da muke  ciki ba zai iya guje wa abubuwan da suke sanya bacin rai ko fushi ba. Idan haka ne, me ya dace mu yi […]

Matakan kare kai daga yawan bacin rai
Matakan kare kai daga yawan bacin rai

Fushi ko bacin rai na daya daga cikin wasu dabi’u da Allah subhanahu wata’ala ya halicci dan Adam da su. Shakka babu muddin dan Adam yana raye a wannan duniya da muke  ciki ba zai iya guje wa abubuwan da suke sanya bacin rai ko fushi ba. Idan haka ne, me ya dace mu yi a duk lokacin da muka ji ranmu ya baci? Akwai wani bawon Allah da ya turo mini sako kamar haka:
“Annuree, na san za ka yi mamaki me ya sa mu Hausawa muke da hassada, har wanda ake yi wa hassadar ya gane? Abokai na suna munafuncina in na gansu raina baci yake yi. Abokan suna shaye-shaye in na gansu suna yi raina baci yake yi. Makwabtana ba su da aikin yi, sai munafunci in na gansu suna yi raina baci yake yi. In na je wata unguwar na dawo ina shigowa unguwarmu raina baci yake, saboda hassada da gaba da kiyayya da munafunci sun yi wa manyan uguwarmu yawa. Basa taimako ko kadan. Kuma In na ga yaran talakawa ba wanka, ba kaya masu kyau a jikinsu, ba ci, ba sha, ba karatu ba tarbiya, ba gun kwana mai kyau raina baci yake .
Ga ‘yan matan unguwarmu girman kai ya yi musu yawa, in na gansu raina baci yake. Ka ba ni shawara Annuree kodayaushe sai na ga wadannan abubuwa.”
Idan muka lura da wadannan furuci na wannan bawan Allah za mu fahimci cewa a mafi yawan lokuta mu muke bayar da kofa har fushi ko bakin ciki ya rinjaye mu. Kamar wannan bawan Allah akwai mutane da yawa wadanda suka zabi kasancewa cikin bakin ciki ko bacin rai kan abin da bai shafe su ba. Hakazalika mutane kan zabi zama cikin bacin rai akan matsalar da za su iya shawo kanta in har sun yi niyyar hakan. Yawan bacin rai yana da muguwar illa ga lafiyar jikin dan Adam. Kimanin karni biyu da suka wuce, wani shahararren marubuci dan kasar Amurka mai suna Ralph Waldo Emerson ya taba cewa:
“Kowane minti daya da kuka kwashe kuna fushi, kun yi asarar dakika 60 na farin ciki.”
Saboda haka yana da kyau mu yi kokari wajen shawo kan yawan bacin rai da muke yi. Haka kawai za ku ga mutum yayi kusan mako guda yana bata rai don kawai wani dan siyasa wanda bai taba tsinana masa komai ba ya canja sheka, daga wata jam’iyya zuwa wata daban, ko kuma don kulob din da yake goyon baya sun kasa lashe wasa. A sanadiyar haka ma wani sai ku ga ya yi bugun zuciya ya mutu.  Saboda Allah mece ce ribar? Domin shawo kan matsalar yawan fushi ko bacin rai yi la’akari da wadannan shawarwari da ke kasa:
1. Tambayi kanka: A duk lokacin da ka ji ranka ya baci, to, yana da kyau ka tambayi kanka mene ne dalilin bacin ran? Wane abu ne mai muhummanci ka rasa da ya zama maka tilas ka bata rai? Idan ka yi kokarin amsa wadannan tambayoyi za ka gane dace ko rashin dacewar fushin da kake yi. Da zarar ka fahimci ai lokacin da Tanko yake APC bai taba tsinana maka komai ba, toh ba za ka bata ranka don ya koma PDP ba.
2. Me kakeso? Idan har kana tare da abn da bai amfaneka ba, mene ne dalilin bata rai idan ka rasa abun? Da yawan mutane babu alkibla, wasu ba su san abin da suke so ba, ballantana abin da ba sa so. A kodayaushe ka kasance ka san alkiblar da ka dosa. Hakan zai taimaka wajen kare ka daga shiga cikin ruwan bacin ran da ba zai tsinana maka komai ba.
3. ware wa kankawasu lokuta: A maimakon kullum kana cikin jama’a ana hayaniya, ko kana sanya ido kan harkokin wasu, ya kamata ka rika ware wa kanka wasu lokuta da za ka zauna kai kadai, domin samun natsuwa, tare da tunanin mafita ga dukkan matsalolin da kake fuskanta. Ba wai don ka ga wani yana ciwon kai sai ka yi wuf ka hadiye Panadol a madadinsa ba.
4. Mece ce matsalar? Idan har ba a gano bakin zaren ba, ai dinki ba zai yiwu ba. A lokacin da ka gano bakin zaren, sai ka yi kokarin dinke barakar da ke tsakaninka da farin cikin ranka. Yana da illa babba mutum ya zabi zama cikin bakin ciki, maimakon nemo mafita daga matsalar da yake fuskanta.
5. Illar bacin rai: Da yawan mutane suna afkawa cikin halin fushi da bacin rai cikin sauki. Tsalle daya zai jefa ka rijiya, amma sai ka yi dubu ba ka fito ba. Da yawan mutane ba su san illar yawan fushi da bacin rai ke haifarwa ba. Idan mutum na cikin halin bacin rai, toh duk abin da ya aikata ba zai taba zama mai kyau ba.
6. Karatun Alkur’ani: Karantawa ko sauraron karatun kur’ani yana yaye bakin ciki da sanya wa mutum natsuwa a zuciya. Baya ga ladar da za ka samu wajen sauraro ko karanta shi, za ka samu damar dinke barakar da ke tsakaninka da farin cikin ranka. Allah yasa mu zamo masu bai wa Alkur’ani hakkinsa kamar yadda ya dace
7. Tuna da wani abin dariya da kataba ji: Yana da saukin share bacin rai idan har za ka iya tuno wani abin dariya da ka taba gani, ko kuma ka taba ji a baya. Idan ma ba ka taba ji ba, ya kamata ka nemi littattafai na nishadantarwa ka karanta su, don samun natsuwa. Hatta jaridun da muke da su, musamman jaridar Aminiya takan ware wani fili, musamman don nishadantar da masu karatu.
Allah ya sa mu dace.

Daga: Naseeru Taneemu Annuree (NTA)
Mataki na 200 a Tsangayar Koyon Aikin Jarida, da ke Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50

Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 30 a Borno

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya