Matakan kare muhalli daga ambaliyar ruwa
Allah ya kaimu shekara ta juyo, bana ana shan ruwa da bakin kwarya! Abin da yasa wasu masana yanayi ke gani wasu wuraren ma sai an yi ambaliya, kamar yadda aka fara yi a yanzu. Damina kan zo da sauyin iska daga Kudu zuwa Arewa, inda za a fara da yawan kadawar bishiyoyi. Yanayin na […]
Allah ya kaimu shekara ta juyo, bana ana shan ruwa da bakin kwarya! Abin da yasa wasu masana yanayi ke gani wasu wuraren ma sai an yi ambaliya, kamar yadda aka fara yi a yanzu. Damina kan zo da sauyin iska daga Kudu zuwa Arewa, inda za a fara da yawan kadawar bishiyoyi. Yanayin na sa a saurari zuwan ruwa, inda ake iska mai dadi da dare, ko kwadi kan yi maraba da wannan yanayin.
Ruwa na daya daga cikin abubuwan da suka fi komai muhimmanci a rayuwa. Ruwa na tsaftace muhalli, ya wanke gine-gine. Ya cike ramukan da ba a cike ba, ciyayi su cika ko’ina ka ga gari ya zama kore. Manoma su sami damar noma da girbi, inda har yara kan noma gonakinsu a lokacin hutu, ba sai an debo ruwa ba, sannan abinci ya yi arha!
A tashin farko ita kanta kasar na fama da kishirwa, shi yasa da an yi ruwa sai ka ji wani sabon zafi na fitowa daga kasa, kafin ta jiku wajen watan Auguta, kamar yanzu kasar ta koshi! da ganin hadari daya yake da saukar ruwa wani lokacin ko ba hadari sai ka ji yaf-yaf-yaf ana ruwa! Ko a wuni ana marka-marka, yayin da hakan ba ya zama cikas a Kudancin kasar nan, inda cikin ruwan za ka iske masu tallar biredi ko kanikawa sun fito, masu sayar da jarida na nasu harkar a gefen titunan, musamman don an shirya wa yanayin.
Damina kan zo da barazanar ambaliyar ruwa, musamman domin mutane na toshe magudanan ruwa da ledoji ko ta hanyar zuba shara a kwata, ko ma su kirkiro ambaliyar ta hanyar gina gidaje a hanyar ruwa! Masana yanayi suna gano cewa a kwananan a bisa sauyin yanani, za a rika yin ruwa mai yawa na tsawon lokaci a inda ba a saba ba, musamman domin akwai kankarar dake narkewa a bisa dumamar yanayi. Rashin shirin tunkarar haka na karfafa ambaliya, sannan akwai matsalolin sare bishiyoyi don wasu bukatu, tare da sauya wa muhallin fasali don wani dalilin da ka iya zama bazarana ga mutane.
Ambaliyar ruwa bala’i ne, domin bai tsaya akan kashe mutane da dukiyoyinsu ba, dabobi basu tsira ba, gonaki, gadoji, tituna da ita kanta kasar, kai ko madatsun ruwa kan barke su kara dagula yanayi da tabo, kuma akwai yiwuwar bakewar cuttutuka a lokacin ambaliyar ruwa, bugu da kari ruwan kan gurbace da najasa, kuma ya lalata karafa da takardu, ruwa ya shiga tiransfoma a dauke wuta kuma a gaza kunna janareto, ambaliyar ruwa na jagwalgwala komai.
Ya kamata hukumomin gine-gine da kulla da muhalli a jihohi su rika fitar da hanyoyin ruwa kafin a raba filaye tare da sa idon wajen bin ka’idar yadda aka tsara hanyoyi a gaba da bayan gidan, kar wani ya shiga gonar wani. Irin jagwal din da ake a sabbin ungwanni kan kawo minista, kwamishina ko gwamnan da zai yi rusau! Ta yadda daga bisani za a ji dadin gyaran da za a wa mazaunin, bayan an yi rushe-rushe tare da wa wasu wurare kwaskwarima.
Radadin ambaliyar ruwa ya wuce barnar lokaci guda, akan dauki tsawon lokacin kafin a daidaita lamura a yadda suke, kuma a kashe dukiya mai yawan gaske, sannan ambaliya kan zama sanadin tsiyacewar mutane ko kasashe. Ya kan takura wa talakawa, kuma ya mayar da attajiri talaka! barnar ambaliyar ruwa na sa mutane su rasa ‘yan uwa, gidaje da dabobi, balle takardun banki, takardun filaye ko satifikate dinka! Kuma sai shekara ta zagayo ba a gyara matsuginin mutanen ba, sai a jibge su a wata firamare ko ofishin jam’iyya a raba masu alakoro kafin a manta da su!
A wasu kasashe akan yi amfani da kwamfuta wajen bincike, lura da gane lokacin da yanayin ruwan da za a yi, kuma dama an tsara mazauni a yadda ruwa ba zai kwanta ba. A haka an rage matsalar ambaliyar, ba ruwan ruwa da cewa sai biranen bakin gaba, ko a Hamada sai a yi ambaliya. Kuma akan yi ceto da helikwafta, karnkan da aka ba horo da asibitocin gaggawa! Sannan wani ikon Allah shi ne an fi samun ambaliyar ruwa a kasashen da suka fi ci gaba! musamman a kasashen nahiyar Asiya kamar Caina, Indiya, Malesiya, Indonesia, Thailan, duk da cewa kasashen Turai ma kan fuskanci barazanar, kuma ba a bar Amurka a baya ba, inda wani lokacin sai dubunnan mutane su mutu, kuma a yi asarar biliyoyin daloli a dalilin wannan barazana.
Ruwa kan zama cikas ga matafiya, musamman masu babura, ruwa kan yi yawo da mota a hanya ko ma ya ture ta gefe, haka ya kifar da jiragen ruwa. Ana soke tashin mota daga tasha, inda matafiya ke kukan sauya lokutan tafiya. Masu motoci kan yi tafiya a hankali don gudun zamewa, ko fadawa cikin rami, ko kar motarka ta tsaya cikin dare, a lokacin damina mutane kan tashi daga sana’o’insu da wuri.
Akan ji dadin bauta a lokacin damina, domin lokacin da ruwa ke sauka na daya daga cikin lokutan da aka fi karbar addu’a, lokaci ne mustajaba. kuma ba sai an nemi ruwan alwala ba! Sannan lokacin ya kasance lokaci mai tsawon watanni, ana yin hutun ‘yan makaranta yayin da wadansu kan taimaka wa iyayensu da aiki a gona. Akan sami sauyin lokacin wasu bukukuwa ko tarruruka don ruwa ya hana a je akan lokaci ko a taru, amma albarka na sauka daga sama!
Da an iya siyasa da an ci ribar damina, domin ‘yan siyasa za su iya amfani da damina wajen jan hankalin jama’a, ta yadda za a raba wa yara ‘yan makaranta da mata da tsofaffi da manyan mutane miliyoyin lemar jam’iyya ko jam’iyya mai mulki ta yi amfani da wannan tsarin don kariya daga zafin rana ko dukan ruwa!
Damina na da barazana ga wanda bai kulla da muhallinsa ba, musamman game da iskar da ake yi a farko-farkon faduwar ruwan sama, da lokacin da ake ruwan har bayan an yi ruwan wani kan kwana da yunwa a dalilin damina! sai a shirya da dan kuli-kuli a daki don kar a kwana da yunwa. Sannan hadari kan hadu ba tare da sanarwa ba! Ya kamata a hankaltu a ilimintar da mutane game da damina.
Buhari Daure
+2347035986444
[email protected]