Matakan lura da ciki bayan haihuwa(2)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba bayanin da muka fara kawo muku a makon jiya kan matakan lura da ciki bayan haihuwa. Allah Ya sa bayanin ya amfanar da masu bukatarsa, amin. Motsa jiki ta hanyar YogaIdan ba kya so ki rika tafiya a matsayin motsa jiki, to za […]

Matakan lura da ciki bayan haihuwa(2)
Matakan lura da ciki bayan haihuwa(2)

Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan fili. Ga ci gaba bayanin da muka fara kawo muku a makon jiya kan matakan lura da ciki bayan haihuwa. Allah Ya sa bayanin ya amfanar da masu bukatarsa, amin.

Motsa jiki ta hanyar Yoga
Idan ba kya so ki rika tafiya a matsayin motsa jiki, to za ki iya motsa jikinki ta hanyar Yoga. Wannan ya kunshi motsa dukkan gabobin jikinki, ta hanyar nade su, ko lankwasa su, ko kuma jujjuya su. Idan har za ki iya, to yana da kyawu ki dora kafarki a wuyanki, ko ki taba keyarki da tafin kafarki. Hakan zai sanya jijiyoyin jikinki sakewa, sannan cikinki ya koma kamar yadda yake kafin ki samu juna biyu.
Ninkaya
Ninkaya tana taimakawa wajen mikar da jijiyoyin jiki, motsa jiki ce da ba ta bukatar hada abu mai nauyi, kodayake yana da kyawu ki rika ninkaya a lokacin da kike da juna biyu ma. daga abu mai nauyi ma na kare wadda ta haihu daga ciwon rashin kwarin kashi da ake kira osteoporosis. Ninkaya tana da fa’ida ga wadda ta haihu domin tana sanya jikinta ya samu kuzari. Za a iya motsa jikin ninkaya a kan taburma ko da karfen motsa jiki mai duna dumbbells. Yadda za a motsa jiki da dumbbells kuwa shi ne, za ki samu dumbbell guda biyu, sai ki shiga cikin ruwa da su, sannan ki rike su a hannu, kafin ki rika ninkaya. Za ki iya ninkaya a kan taburmar da ake amfani da ita wajen ninkaya a cikin ruwa
Motsa jiki na Kegel
Motsa jikin Kegel na da matukar amfani ga wadda ta haihu, domin zai taimaka cikinta ya koma daidai. Yadda ake wannan motsa jikin kuwa shi ne, za ki kwanta a kan taburma, sai ki mike hannuwanki a kan taburmar, daga nan ki ki nade kafafunki, inda gwiwowinki su kalli sama. Bayan nan ki ja dogon numfashi, sannan ki sake. Za ki iya dora yatsun kafafunki a kan taburmar, sannan ki rika tura kafafunki sama, kamar yadda mutum yake yi idan zai yi dagel-gel. Sannan za ki iya nade hannuwanki a bayan wuyanki, sannan ki rika tura kanki da tafin hannuwanki. Za ki iya rike idanun sawayenki, sannan ki rika turawa da kuma dawo da kafafunki. Wannan nau’in motsa jiki na sanya jijiyoyin kwankwaso sakewa.
Tafiya
Tafiya na mikar da jijiyoyin jiki, kuma na sanya a rage kiba, motsa jiki mafi a’ala ga wadanda suka haihu ma shi ne tafiya. Tafiya na sanya daddadar iska ta shiga jiki, jijiyoyin kafafu su sake, sannan tana taimaka jiki gaba daya don ya samu lafiya. Abin da ake bukata shi ne, ki samu takalman kambas ko sandal masu kyawu.
Daga karshe ina fata masu juna biyu ma za su rika motsa jiki, domin hakan zai taimaka musu wajen haihuwa, zai kuma taimaka musu bayan sun haihu, ga wadanda suka haihu kuma ina fata za su rika motsa jikinsu, don cikinsu ya koma kamar yadda yake kafin su samu juna biyu. Allah Ya taimaka, amin.