Matakan lura da hannuwa
Mata da dama sukan mayar da hankali wurin lura da jikinsu, sannan su manta da hannuwansu, sai ka samu komai nasu da kyawu face hannuwansu, wadansu ba sa mayar da hankali wajen lura da hannuwansu ne kasancewar da su ne suke yin dukkan ayyukan gida. A wannan makon mun kawo miki yadda za ki lura […]
Mata da dama sukan mayar da hankali wurin lura da jikinsu, sannan su manta da hannuwansu, sai ka samu komai nasu da kyawu face hannuwansu, wadansu ba sa mayar da hankali wajen lura da hannuwansu ne kasancewar da su ne suke yin dukkan ayyukan gida. A wannan makon mun kawo miki yadda za ki lura da hannuwanki don su yi laushi:
1. Da farko dai ki rika wanke hannuwanki da ruwa mai tsabta akai-akai. Za ki iya amfani da sabulan da ke dauke da sinadaran man zaitun da jojoba. Idan za ki wanke kwanuka kuma ya kamata ki yi amfani da safar hannu, don samun kariya daga sinadaran da ke cikin omo, wadanda za su sanya hannuwanki bushewa ko tsagewa.
2. Ki guji amfani da ruwan zafi wajen wanke hannuwanki.
3. Idan kika shafa hadin ruwan siga da man zaitun a hannuwanki zai cire miki matattun kwayoyin halittar da ke hannuwanki. Bayan kin shafa hadin a hannunwanki za ki bar shi zuwa zuwa minti 2. Daga nan sai ki wanke su da ruwa mai dimi.
4. Za ki iya shafa mayukan da ke sanya jiki laushi a hannuwanki. Za ki iya shafa man kade ko sinadarin bitamin B ko retinol.
5. Idan kuma hannuwanki sun tsattsage sai ki shafa musu man hannu wato ‘conditioning hand salbe’, yana nan kamar man baseline.