Matakan magance warin jiki
Mata da dama sukan samu kansu cikin tsomomuwa sakamakon warin jiki, musamman sun gwada wadansu hanyoyin da za su magance warin jiki, amma abin ya ci tura. Wata mata ta taba turo mini sako cewa ta rasa dalilin da ya sa jikinta yake wani irin wari duk da cewar tana wanka sannan tana shafa mai. […]
Mata da dama sukan samu kansu cikin tsomomuwa sakamakon warin jiki, musamman sun gwada wadansu hanyoyin da za su magance warin jiki, amma abin ya ci tura. Wata mata ta taba turo mini sako cewa ta rasa dalilin da ya sa jikinta yake wani irin wari duk da cewar tana wanka sannan tana shafa mai. Don haka a wannan makon na zo muku da bayanin matakan da za ku bi don jikinku ya rika kamshi mai dadi.
Tufafi
Yana da kyau ku rika wanke tufafinku da sabulan da suke da kamshi mai dadi, sannan kada ku rika zama da kayan da suka yi datti, kana idan kun shiga rana da kaya idan kun dawo sai ku shanya su don su sha iska, idan suka sha iska sai ku shigar da su daki, domin idan kuka shigar da su haka za su rika wari, wanda hakan zai sanya ya rika damun daki ko kuma akwatin da aka ajiye su. Ku guji maimaita kaya ba tare da kun wanke su ba, dalili kuwa shi ne, idan kun yi gumi yakan makale a tufafin da kuka sanya.
Turaren Hammata
Yana da matukar muhimmanci ku rika sanya turaren hammata, ba wai sai za ku fita unguwa ba, har a gida domin hakan zai taimaka muku ku rika bayar da kamshi mai dadi. Yawan gashi a hammata yakan haifar da gumi yayin da gumin kuma ya haifar da warin jiki, don haka yana da kyawu ku aske gashin hammata. Ba kowane turaren hammata za ku saya ba, a’a, ku zabi wanda zai dace da sabulun da kuke wanka ko turaren da kuke fesawa da kuma ire-iren man da kuke shafawa, don kada ya bayar da kamshin marar dadi.
Ya yin shafa turaren hammata yana da kyawu ku game dukkan hammatarku da turaren, sannan ba sau daya kawai za ku shafa ba, ku shafa kamar sau uku ko hudu a rana.
Sinadarin binegar
Ku samu sinadarin binegar kadan, sannan sai ku gauraya shi da ruwa, daga nan ku tsoma auduga a ciki, sannan ku rika goga audugar a hammatarku. Sai dai ba duka mata ne hakan yake zama hanyar magance musu warin jiki ba. Idan bayan kun gwada hakan ba a samu canji ba, sai ku hakura. Ba a so ku rika shafa sinadarin binegar a hammatarku idan har kun aske ta.