Matakan rabuwa da zinar hannu (2)
Assalamu alaikum wa rahamatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan batutuwan da za su zo cikinsa, amin.Ga ci gaban bayani kan hanyoyin da matasa za rabu da zinar hannu. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da […]
Assalamu alaikum wa rahamatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan batutuwan da za su zo cikinsa, amin.
Ga ci gaban bayani kan hanyoyin da matasa za rabu da zinar hannu. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Mataki na 5: Shirya Kayan Yaki
Babbar matsalar dan Adam a bayan kasa ita ce: kasawarsa ga kai harin ramuwa ga shaidan, kamar yadda kullum shaidan ba ya kasa kawo harin gare shi. dan Adam ya san shaidan makiyinshi ne, ya san ba shi da wani buri ko wata bukata irin ta ya ga ya halakar da shi ya fada cikin fushin mahallicinSa, yana sane da irin harin da shaidan din kullum yake yawan kawo masa, amma ba ya kokarin shirya kayan yaki balle har ya mayar da harin da shaidan din yake kai masa a kullum, kuma ba ya kokarin gina ganuwar da za ta kare shi da harin da shaidan din yake kawo masa. Ga matashin da ke kokarin rabuwa da wannan kazamar dabi’a, dole sai ya gina katuwar ganuwar da za ta kare shi daga harin da shaidan ke kawo masa kodayaushe; zai iya yin wannan ta amfani da mataki na 2 da na 3 da bayaninsu ya gabata wancan sati; watau gyaran zuciya da inganta imani. Kayan yakin da za a iya yakar shaidan da su ta hanyar yin abubuwan da za su hana shaidan din sakat da kuma hana masa abinci da abin sha; sutura da kwanciyar hankali: za a iya yin haka ta wadannan hanyoyin:
1. Yin bisimillah kafin gabatar da kowane irin abu komai kankantarsa ko rashin muhimmancinsa, kamar in za a zauna ko za a tashi; ko da in za a dauki wani abu, in za a bude ko rufe kofa ko tagar, da sauransu. Duk abin da aka fara shi da bismillah, to shaidan bai isa ya sa hannu ciki ba balle har ya iya tasiri a cikinsa.
2. Yin addu’ar fita daga gida duk lokacin da za a fita:
‘Bismillah, Tawakkaltu alallah, wala haula wala kuwwata illa billa; Allahumma inni a’uzu bika an adilla au udal, au azilla au uzal, au azlima au uzlam, aw ajhala aw yujhala ilayy.’
shaidan ba zai iya samun wani iko a kan mutum ba har ya dawo gida; kuma ana isa wajen da za a je, ko da wajen aiki ne ko wani wajen, nan ma sai a yi wannan addu’a sau 3:
‘A’uzu bi kalimatillahi tammati min sharri ma khalaka.
To shaidan ba zai iya wani iko ga mutum ba har ya bar wannan wajen.
3. Ana komawa gida kuma sai a karanta wannan addu’a:
‘Bismillahi walajna, wa bismillahi kharajna wa ala Rabbina tawakkalna.’
4. Sannan in za a ci abinci ma sai a yi Bismillah; In za a zubar da kashi bayan an tsotse shi, ko wani abinci, sai a yi Bismillah, to Musulman aljanu ne kadai za su iya cin wannan kashin ko abincin.
5. Annabi SAW ya ce duk wanda yake bismillah yayin shiga da kuma in zai ci abinci, shaidan zai ce yau ba a abinci gare mu kuma ba mu da wurin kwana. Watau ke nan duk abinci da aka yi bismillah yayin da za a ci shi, shaidan ba zai ci shi ba; kuma idan aka yi addu’a yayin shiga gida, shaidan ba zai kwana a cikin irin wannan gidan ba.
6. Yawan neman tsarin shaidan a kodayaushe, ta hanyar fadar ‘A’uzu Billahi minash-shaydanir-rajim.’ Musamman duk lokacin da matashi ya ji muguwar sha’awar son yin zinar hannu ta motso masa, sai ya yi ta maimaitawa har sai ya ji ya rabu da ita. In kuma har ya kasa daurewa sai ya yi din, to sai ya yi fadar wannan addu’a tare da bismillah, a cikin zuciyarsa, lokacin da yake yi din.
7. Yawan karatun kur’ani da yawan sauraren karatun kur’ani musamman Suratul Bakara, sauraren kiran Sallah, duk abubuwa ne da ke korar shaidan, su ta da masa hankali. Da fatan Allah Ya ba mu ikon dagewa ba fashi, amin.
Mataki Na 6: Sarrafa Tunani
Duk lokacin da matashi ya ji son aiwatar da zinar hannu ya muntsile shi, sai ya yi ta maza ya dauke hankali da tunanin shi daga wajen, ta hanyar yin wani abu da dole tunaninsa ya karkata daga tunanin zinar hannu; misali; in a zaune ake sai a mike tsaye ko a yi tafiya; ko a kama yin wani aiki; hakan nan kuma matashi na iya sa dankon robali a hannunshi wanda zai iya ja da karfi ya ji zafi, ko ya muntsini kansa, ya gamtsara wa yatsansa cizo; duk don kubutar da kansa fada wa cikin aikata wannan mummunan aiki.