Matakan rabuwa da zinar hannu (3)
Assalamu alaikum wa rahamatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan batutuwan da za su zo cikinsa, amin.Ga ci gaban bayani kan hanyoyin da matasa za su bi don rabuwa da zinar hannu; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya […]
Assalamu alaikum wa rahamatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan batutuwan da za su zo cikinsa, amin.
Ga ci gaban bayani kan hanyoyin da matasa za su bi don rabuwa da zinar hannu; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Mataki na 7: Magance Fitinanniyar Sha’awa
Da yawan samari masu aikata wannan dabi’a na kukan cewa matsananciyar sha’awa ce da ta yi masu yawa ke kai su ga aikata wannnan kazamar dabi’ar. To ga hanyoyin magance fitinanniyar sha’awa:
1. Sha’awa dai shauki ce kamar sauran shau’uka na ma’aikatar hankali, don haka tana bukatar kuzari kusan uku kafin kasancewarta. Mai fatan ya rabu da wannan dabi’a sai ya sa kansa cikin sha’anoni da ayyuka masu yawa, musamman na neman lada da falala ta yadda ba ma zai samu lokacin tsunduma cikin tunane-tunanen alfasha ba. Wata karin magana ta Turawa na cewa mutum mai albarka shi ne wanda yake ayyuka da yawa da rana har ba su barin ya shiga damuwa, kuma tsananin gajiya ya hana shi shiga damuwa da daddare. Don haka matashin da bai aikin karfi, sai ya fara, wanda ke yi kuma sai ya kara, Matashi ya tarkato aikin da ba ya son yi, ko wanda yake ganin ya fi karfin yi, (kamar su gyaran kwatar cikin Unguwa), a hankali zai fara son abin nan, in kwakwalwa ta kasance kodayaushe akwai abin da ke gabanta, a hankali za ta kone kuzarin sha’awar da ya yi yawa; domin ba kuzarin da ya kai kuzarin sha’awa karfi, don haka in ya yi yawa ko in ba a amfani da shi ana iya juyar da shi a cimma wani burin na rayuwa maimakon a yi ta barnatar da kuma asarar sa a banza ba. Don haka matashi ya kiyaye zama ba ya yin komai, domin a irin wannan lokacin ne shaidan kan lallabo ya tsirar da tunanin sha’awa cikin zuciya, in ko mutum na aiwatar da wani aiki kusan kodayaushe, to ko shaidan ya tsirar masa da tunanin sha’awa, to wannan tunanin ba zai yi tasiri ba. Ko kallo ne mutum zai yi, to ya fi masa alheri ya kalli abubuwan karuwar ilimi ko wadanda za su caza masa kwakwalwarsa, ba fina-finan labaran soyayya ba, ko na kide-kide da wake-wake, domin wadannan duk wasu abubuwa ne masu assasa ruruwar wutar sha’awa cikin jiki.
2. Yana da kyau ga mai fama da matsananciyar sha’awa ya fahimci cewa, sha’awa ba komai ba ce illa daya daga cikin al’amuran gudanarwar jikin dan Adam da Allah Ya halitta shi da su. Kamar yadda wani ya fi wani tsawo, wata ta fi wata tsawon gashi, wani da saurin fushi wani kuma da sanyin zuciya, to haka sha’awa ta bambanta tsakanin mutane ta fuskoki daban-daban. Kamar yadda mai tsananin fushi Allah Ya hore masa iko da damar dannewa da hadiye fushinsa, to haka ma mai tsananin sha’awa yana da cikakken ikon da zai danne sha’awarsa, ya kasance sai lokacin da ya bukace ta ne kadai za ta yi tasiri a cikin rayuwarsa da harkokinsa na yau da kullum. Kada mutum ya ce ‘ai ni haka Allah Ya yi ni!’ don haka ya doge da sabon Allah Yana cutar kansa, Allah SWT bai halitta barna cikin ko daya daga cikin halittunsa ba, sai dai shi abin halittar ya jawo wa kansa barna da abin da Allah Ya halitta masa, mu lura zuwa ga shukokin da Allah Ya azurta mu da su, ko wace shuka Allah ya aje ta a mafi dacewar waje da yanayinta, kuma ya hore mata abubuwan da za ta girma ta yadu a wannan wajen. Don haka komai Allah Ya ba mutum, shi ne daidai abin da zai yi amfani da shi ya girma, ya yadu, ya kuma yi nasara a duniyarsa da lahirarsa. Haka kuma tsananin sha’awar da Allah Ya ba wani na iya zama wata jarrabawa ce da Allah Ya yi nufin Ya jarabci bawanSa da ita, in mutum ya yi hakuri ya jure, Allah zai saka masa da mafi kyawon sakayya.
3. Duk lokacin da sha’awa ta motso wa mai fama da ita, to ya san yadda zai yi ya karkatar da tunaninsa daga wannan sha’awar, duk lokacin da wannan igiyar tunanin ta bijiro wa mutum, to ya yi sauri ya tsinke ta, ta hanyar saka wani tunanin daban cikin zuciya wanda ba shi da nasaba da sha’awa, misali, sai mutum ya yi wa kansa wani abun da zai sa dole ma’aikatar hankalinsa ta saki wancan tunanin ta koma ga abin da ke faruwa a jikinsa a wannan lokacin, dole kwakwalwa take-yanke ta bar wancan tunani ta koma ga na jin zafi, domin kwakwalwar dai guda daya ce, zai yi wuya ta saurari abubuwa biyu masu karfi a lokaci daya!
Zan dakata a nan sai sati na gaba in Allah Ya kai mu. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.