Matakan samar da zaman lafiya ga al’umma
Rayuwa cikin zaman lafiya ita ce rayuwa mai dadi da sanya karsashi. Zaman lafiya a rayuwa shi ke haifar da lafiyar ita kanta da ci gaba da nasara da daukaka da dukkan wani alheri na rayuwar duniya da lahira. Ba a samun ci gaban rayuwa a duk inda ba zaman lafiya, domin yana haddasa gaba, […]
Rayuwa cikin zaman lafiya ita ce rayuwa mai dadi da sanya karsashi. Zaman lafiya a rayuwa shi ke haifar da lafiyar ita kanta da ci gaba da nasara da daukaka da dukkan wani alheri na rayuwar duniya da lahira.
Ba a samun ci gaban rayuwa a duk inda ba zaman lafiya, domin yana haddasa gaba, kiyayya, keta, hassada da tsoro kuma yana ruguza amana, yarda da kaunar da ke tsakanin al’umma. Duk muhallin da ke fama da rashin zaman lafiya, ba yadda za a yi a samu wani ci gaba a tare dashi.
Ba sai mun yi dogon bayani a kan illolin da ke tattare da rashin zaman lafiya ba. Duk wata halitta da Allah Ya yi ba wadda ke kaunar rashin zaman lafiya. Duk da sanin illolin rashin zaman lafiya da dan Adam ya yi amma sai ka tsince shi yana cin karo da wani sanadi da zai kai shi ga rashin zaman lafiya. Amma kuwa ya kamata mutane ko al’umma mu gane, mu kara kulawa wurin kiyaye zaman lafiyarmu, domin dadi da alfanu da tasirin da ke da shi a rayuwarmu.
Me zai hana mu maida hankalinmu ga matakan da za su samar mana zaman lafiya a cikin zamantakewarmu ta yau da kullum, ko mu ce rayuwar mu ga baki daya.
Akwai matakan wanzar da zaman lafiya kala-kala a cikin al’umma da muhalli daban-daban, domin al’adunta da dabi’unta mabanbanta da muke da su, duk da haka akwai matakan wanzar da zaman lafiya da suke da tasiri a cikin kowace irin kabila ko al’umma, sai dai ya rage wa al’adarsa ta nuna masa ta yaya zai gabatar da su ga al’ummarsa? Matakan su ne kamar haka:
So ko Soyayya: Masu azancin magana sun ce ‘so shi ne rayuwa.’ Me ya sa suka ce haka? Domin Allah bai halicci wata alaka ko hulda mai karfi fiye da soyayya ba. Harwayau, ba abin da ya samar wa duniya rayuwa cikin jin dadi da annashuwa in ban da soyayyar da ke gudana a cikinta. Yau da a ce kowa makiyin dan uwansa ne, ba soyayya a tsakanin juna, da ba ci gaban rayuwa ta kowace irin hanya, domin ba za a samu auratayya ba, balle zamantakewa.
‘So hana ganin laifi.’ Haka ne, ai duk wanda kake so ba ya laifi a gunka. Ko ya yi ma bai cika yin tasirin haushi ko zafi a gare ka ba, don haka wannan rashin ganin laifin ba karamin zaman lafiya yake shukawa ba.
Kuma mu lura mu gani, duk inda ba zaman lafiya to soyayya ce ta yi balaguro. Matukar soyayya na wurin ba za ta bari husuma ta zo wurin ba.
Alheri ya tabbata ga al’ummar da suka bari so ya ratsa zukatansu kuma kaico ga al’ummar da ta kasa haskaka wa jama’arta hasken so mai amfani.
Hakuri da Juriya: ‘Hakuri maganin zaman duniya.’ Gaskiya duniya tana da wuyar zama kwarai da gaske amma kuma mahakurci ne ke iya rayuwa cikinta, a cikin kowane hali da yanayi, ba tare da kunci ko gazawa a tare da shi ba. Duk mai hakuri ba za ka same shi da tada husuma ba, balle ma ta kai shi ga haddasa rashin zaman lafiya ga kansa ko ga al’ummarsa.
Mu duba mu gani, yadda rashin hakuri yake kai mu ya baro mu. Kullum mu ne hasarar dukiya da muhalli, kai har ma da rayuka saboda rashin hakurinmu. Da zan yi hakuri, kai ka yi hakuri, da duk mun zauna lafiya. Mu rika hakuri da junanmu. Allah Ya san dalilin da ya sa ya yi mu a tare. Mu daina barin rashin hakuri yana yi mana hasarar zaman lafiyarmu. Mu koya wa kanananmu hakuri da junansu a zamantakewa, ko a samu zaman lafiya a zamani na gaba.
Kaicon zuciyar da ake zafafa ta da rashin hakuri kuma alheri ya tabba ta ga zukatan masu hakuri.
Yafiya ga Juna:
Aka ce ‘zo mu zauna, zo mu saba.’ Lallai kam zamantakewa ta gaji haka amma bambance-bambancenmu ne ke kawo mana rashin jituwar da ke kai mu ga rashin zaman lafiya da junanmu. Sai dai abin so a nan shi ne ‘yafiya.’ Yafiya na nufin fahimtar kuskuren juna, gyarawa, mantawa da abin da ya wuce na kuskuren. Wanda ya yafe shi ne a saman wanda aka yafe mawa kuma duk mai kulle kofa ga yafewa, to yana bude kofa ne ga rashin zaman lafiya.
Gaba da kiyayya su ne tushen rashin zaman lafiya kuma masu yada su cikin al’umma, su ne suka rikita duniya amma muna iya daukar yafiya domin ceton duniyarmu daga halin da take ciki na tashin hankali da fitintinu.
Me zai hana mu rika yafe wa junanmu? Mu duba tarihi mu ga yadda duniya ta sha wuya a wurin mutanen farko, a dalilin daukar fansa da ya yi ta gudana a cikinta. Duniya ta wahala, ta nakasa, ko yanzu ma a cikin wannan zamanin namu, mu duba yadda daukar fansa yake kawo mana tarnaki ga ci gabanmu. Da za mu dauki matakin yafiya da mun huta.
Tattaunawa da Sulhu: ‘Tattaunawa da sulhu su ne makasan rigima.’ Lallai kam, domin duk inda aka yi nasarar shuka su to rigima ba za ta tsiro wurin ba. Idan ma ita ta fara tsira to ana shuka sulhu rigima za ta fara yaushi, har sai ta mutu domin ba su shan inuwa daya da juna.
Tattaunawa da sulhu ne ke da karfin kama fitina su daure ta, su hana ta motsi kuma su ke da ruwan kashe fitina nan da nan, komai balbalin wutarta.
Tattaunawa da sulhu su ne hanyoyi mafi sauki da dadi domin wanzar da zaman lafiya, domin tattaunawa ce ke halarto da bangaroran rikici wuri daya, a zauna kowa ya fadi abin da ba ya yi masa dadi da dan uwansa a cikin zamantakewarsu. Ta nan ne ake fahimtar matsalolin juna, ta nan ne ake gano bakin zaren warware su da matakan kare sake faruwar su.
Shi kuwa sulhu, shi ne daidaito da maslahar da aka samu a wurin zaman tattanawa da juna. Ma’ana, kowa ya fadi matsalarsa, kowa ya gane matsayinsa, mai gaskiya da marar gaskiya. To wannan shi ake kira da sulhu. Tattaunawa ita ke samar da sulhu mai dorewa.
To wai me ya sa ba mu daukar matakin tattaunawa da sulhu a sahun gaba cikin zamantakewar rayuwarmu, sai dai kullum su ne a baya; bayan dukkan barnar da husuma ke son yi ta yi abinta, an rasa rayuka, an rasa dukiyoyi, an lalata muhalli an koma baya; dukkan illoli an yi wa juna, sannan ake tunowa da sulhu? Wanda da tun farko shi aka tasa a gaba da ba a kai ga hakan ba. Wai sai ka ga mutum yana girman kai wajen fara kiran tattaunawar sulhu. Sai ya manta da alfanunsa a gare shi, na sama masa zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Gaskiya ya kamata mu maida hankali sosai wajen kara wa tattaunawa da sulhu karfi da muhimmanci da kuma yin duk mai yiwuwa wajen ganin sun koma sahun gaba a cikin zamantakewar rayuwarmu, domin sa su a sahun gaban shi ne alfanu.
Daga karshe ina son in kara jan hankalinmu da mu kula da zaman lafiyarmu, mu daina sakaci da shi, mu yi riko da matakan wanzuwarsa da kyau; domin su ne lizamin jan ragamar gudanar zaman lafiya a cikin zamantakewar rayuwar mu ta yau da kullum.
Ya kamata mu sani kuma mu gane cewa idan da soyayya, za a yi hakuri. Idan aka yi hakuri to za a yi yafiya, in kuwa aka yafe, to za a tattauna kuma a samu sulhu.
Ya Allah Ka taimake mu a cikin fafutukar neman zaman lafiyarmu, Ka ba mu sa’ar ganin mun tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a cikin zamantakewar mu ta yau da kullum, amin.