Matakan soyayyar auratayya
Assalamu Alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Matakan Soyayyar AuratayyaSoyayyar auratayya tana da matakai da suke faruwa daya-bayan-daya a tsawon lokacin gudanarta, kuma matakin farko shi ke haifar da na biyu, na biyu ya haifar […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
Matakan Soyayyar Auratayya
Soyayyar auratayya tana da matakai da suke faruwa daya-bayan-daya a tsawon lokacin gudanarta, kuma matakin farko shi ke haifar da na biyu, na biyu ya haifar da na uku, haka dai har zuwa ga cikarta da kammaluwarta. Soyayyar auratayya tana da matakai guda hudu:
1. Magagin kauna: Shi ne farkon aure, lokacin ana cikin giyar so da kauna da sha’awar juna; sai dai wannan magagi zai rika sakinsu a hankali kadan-kadan har wata ran su wayi gari su nemi wannan magagin kauna su rasa. Shi daman magagin kauna wasu sinadaran rayi ne (hormone odytocin) ke sirrance zuciya da shau’ukan jin dadin da ma’aurata kan ji a wannan lokacin, musamman don su tabbatar da kuma saukake faruwar ibadar aure tsakanin ma’aurata, da hakan ya faru kuwa, sun kammala aikinsu, sai su janye su koma bangaren sanya soyayya tsakanin iyaye da dan da suka haifa. Don haka sai ma’aurata su dage wajen ginawa da shuka abubuwan alfanu yayin da suke cikin magagin kauna, don yin hakan zai saukake rikirkicewar da farkowa daga magagin kauna ke haifarwa.
2. Farkawa daga Magagin kauna: wannan mataki ne mai rikirkita rayuwar aure da bice kauna nan da nan daga zuciyar ma’aurata. Bayan farkowar ma’aurata daga magagin kauna, za su ga abubuwa da yawa na tare da junansu, da irin shau’ukan jin dadin da suke ji game da juna duk sun canza, kokarin da suke yi wajen faranta ran juna, yanzu ko rabin shi ba su iya wa, abubuwan da yawa da suke sharewa a matakin farko, yanzu sai ya kasance abin da bai kai ya kawo ba ya sa sun yin jayayya da kace-nace; abuwawan da ya sa suke burge juna ada, yanzu haushi yake ba su. Don haka a hankali sai magudanar soyayyarsu ta tsaya cak ba ta gudana. Kuskuren da ma’aurata kan yi bayan sun farko daga magagin kauna, shine na kasa fahimtar cewa magagin kauna ba itace kadai kaunar da ke tsakaninsu ba, akwai ingantacciyar kuma sahihiyar soyayyar da Allah yake sanyawa a cikin zuciyar dukkan ma’auran juna, tunda sun daina jin fisgar magagin kaunar da sukan ji a matakin farko, to ai shikenan soyayya ta kare, sai dai ayi zaman hakuri ko zaman ‘ya’ya! Wadanda kuma suka kasa yin hakurin, sai abun ya kai su ga mutuwar aure. To mu sani Allah Bai hukunta aure don a yi zaman hakuri ko zaman ‘ya’ya ba, Allah SWT Ya hukunta aure ne don a natsu da juna kuma a zama tufar suturce juna; haka Allah SWT bai son mutuwar aure duk da kasancewarsa halak. Ma’auratan da ke cikin wannan mataki sai su yi kokarin gina sahihiyar soyayyarsu ta asali su mance da waccan magagin kaunar ta matakin farko don samun aminci da natsuwa cikin rayuwar aurensu.
3. An zama daya: wannan mataki yana tattare da kammaluwar amintaka da fahimtar juna tsakanin ma’aurata; yanzu ma’aurata da wuya aji suna kace nace ko jayayya, suna tsananin hakuri da juna da mutunta juna a wannan mataki, kuma suna kokarin kare dukkan hakkokin juna; ma’aurata ba su hantarar juna, jin kyashin juna ko raini; a irin wannan matakin za ka ji Uwargida na tsananin daraja mijinta da girmamashi kamar dai shi wani magabacinta ne ba mijinta ba, Maigida kuma ka ga ba ya son a fadi laifin matarsa ba ya kuma son abin da zai bata mata rai.
4. Kammaluwar Soyayya: Shakuwa da sabo da juna, da gwagwarmayar da ma’aurata suka sha a matakai ukun farko, sun hadu sun gina wata irin soyayya ta musamman tsakanin ma’aurata; suna jin dadin juna kuma ba su fatar rabuwa da juna, ko matsala ta fado masu cikin rayuwar aurensu, tare za su fuskanceta su magance ta domin sun zama daya a ruhi da kuma a sarari.
Wadannan matakai sun bambanta tsakanin ma’aurata bisa ga yanayin silar da ta kulla auratayya tun asali:
• Yawanci ma’aurata magagin kauna ne ke zama sanadin kulluwar auratayyarsu, sai dai wannan magagin kauna ba shi da tsawon rai cikin rayuwar aure, nan da nan zai saki ma’aurata su farka, wannan farkawa ce za ta shigar da su zuwa ga mataki na biyu.
• Wasu ma’auratan kuwa na fara rayuwar aurensu ba so da kauna, ba yarda ba amincewa; ko daya na so daya kuma ba ya so, ko daya ya amince, dayan bai amince ba, misali kamar ma’auratan da aka yi wa auren dole ta bangare daya ko ta duka bangaren. To a irin wadannan ma’auratan, in suka sami fahimtar juna a tsakaninsu, ta iya yiwuwa su tsinci kansu tsundum cikin magagin kauna, watau matakin farko ke nan, kafin daga baya su farko, ko kuma soyayyarsu ta tafi a hankali, suna kara shakuwa da juna, soyayya da kaunarsu na kara zurfi, watau za su fara a mataki na uku ke nan.
• Wasu ma’auratan kuwa yarda da amincewarsu ga juna ne abin da ya yi silar kulluwar aure tsakaninsu; don haka za su fara rayuwar aurensu ba tare da magagin soyayya mai makantar da hankali ba. Irin wadannan ma’aurata sukan fara aurensu ne ba romansiyya cikin soyayyarsu, amma suna kara shakuwa, soyayyarsu na kara ginuwa, su ne ma’auratan da kan fara rayuwar aurensu a mataki na hudu.
• Akan samu ‘yan kadan daga cikin ma’aurata da magagin kaunarsu ba ya bacewa a dukkan tsawon auratayyarsu.
• Wasu ma’auratan kuwa mataki na biyu za su kare auratayyarsu, su kasa samun kwarewar da za ta shigar da su mataki na uku.
• Wata matsalar na iya fadowa cikin ma’auratan da suke mataki na uku har ta yi illar mayar da su matakin rikici, watau mataki na biyu.
• Wasu ma’auratan kuwa a mataki na ukun nan suke kare rayuwarsu ba tare da sun kai ga na hudu ba.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.