Matakan Sulhunta Ma’aurata

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan hanyoyin sulhunta ma’aurata. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin.Ayoyi masu albarka […]

Matakan Sulhunta Ma’aurata
Matakan Sulhunta Ma’aurata

Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar da mu duk bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga bayani kan hanyoyin sulhunta ma’aurata. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma Ya amfanar da su, amin.
Ayoyi masu albarka guda uku daga cikin Suratun Nisa’i sun bayyana matakan da za a bi dalla-dalla don magance husuma da kuma sulhunta tsakanin ma’aurata; ga bayanin wadannan matakai daya-bayan-daya:
Husuma ta bangaren uwargida: In hayakin husumar auratayya ya bullo daga bangaren uwargida, ta yadda take aikata wasu ayyuka masu bata zamantakewa ita da maigidanta; kamar bijire wa umarninsa; fita ba tare da izininsa ba, kin ba shi hakkinsa na ibadar aure, yi masa ayyuka da maganganu na rashin kunya da sauransu: to ga matakan da maigida zai bi don ya kwantar da wannan wutar husumar da ta bullo daga uwargidansa tun kafin ta bunkasa:
“…Kuma wadanda kuke tsoron bijirewarsu to ku yi musu gargadi; (in sun ki) kuma ku kaurace musu a wuraren kwanciya; (sa’annan) kuma ku doke su…”(k:4:34).
Don haka matakan ladabtar da matar da take bijire wa mijinta, ko ba ta yin ladabi da biyayya gare shi guda  uku ne:
1. Gargadi: Maigida zai fara da yi mata nasiha mai shiga jiki cikin siga kyakkyawa; ya tunasar da ita girman Allah da alherin da ke cikin yi maSa da’a da kuma sakamakon azaba da kaskanci da zai sauka a kan duk mai bijirewa ga umarnin Allah (SWT). Ya kafa mata misali da Hadisan Manzon Allah (SAW) da suka bayyana muhimmancin yin da’a ga miji da girman azaba da kaskancin da ke tare da bijire masa cikin duk huldodin rayuwar aure. Misali:
· Manzon Allah (SAW) ya ce duk macen da mijinta ya kira ta shimfidar barcinsu ta ki zuwa, Mala’iku za su yi ta tsine mata har wayewar gari.
· Haka kuma ya ce duk matar da mijinta ya yi fushi da ita Wanda ke Sama (Allah SWT) Zai yi fushi da ita har sai mijinta ya bar fushi da ita, kuma duk ibadunta ba a amsarsu har sai mijinta ya daina fushi da ita.
· Sannan Uwar Mu’uminai A’isha (RA) ta yi kira ga matan wannan al’umma cewa: “Ya ku mata! In da kun san girman hakkin da mazanku ke da shi a kanku, lallai da kowaccenku ta share dattin tafin kafar mijinta da fuskarta!”
· Sannan Annabi (SAW) ya tambayi wata Sahabiya RA: “Yaya kike da mijinki?” Ta  amsa da: “Ina iyakar kokarina gare shi sai dai a kan abubuwan da suka fi karfina.” Sai Ya ce: “Ki kula sosai da yadda kike mu’amala da shi domin shi ne aljannarki kuma shi ne wutarki.”
· Haka kuma Annabi (SAW) ya ce duk macen da ta mutu mijinta yana mai jin dadi da ita za ta shiga Aljanna.
· Kuma ya ce duk macen da ta tsare sallolin farilla biyar, ta tsare farjinta, kuma ta yi da’a ga mijinta za ta shiga Aljannah ta kofar da ta zaba.
To irin wadannan misalan ne maigida zai kwatanta wa uwargidansa; zai kuma iya hada mata da kaset-kaset na wa’azuzzukan malamai daban-daban da littattafai da suka yi bayani da gargadi game da hukuncin bijirewa ga maigida har zuwa lokacin da Allah Ya sa da zuciyarta ta narke, ta yi nadamar abubuwan da ta yi kuma ta tuba ta daina aikata su. Amma in duk nasihohi, gargadi da jan kunnen da aka yi ba su isa ga hana ta aikata ayyukan bijirewar da take yi ba sai a je ga mataki na biyu:
2. kauracewa: A wannan mataki maigida zai kaurace wa matarsa a shimfidar aurensu, ya juya mata baya, ya ki kula ta ko nemanta da ibadar aure. Har sai ta ladabtu ta nemi gafara kuma ta yi nadamar abin da ta aikata sannan maigida ya janye wannan kauracewar. A kula da kyau cewa, a cikin daki a shimfidar gado ne kadai ake kaurace wa mace, amma ba a kaurace mata a cikin sauran bangarorin zamantakewar rayuwar aure; kuma ba a bayyanar da kauracewar nan har sauran jama’a su sani. Kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya fadi cewa daga cikin hakkokin mace a kan mijinta shi ne kada ya kaurace mata sai a cikin gida kadai.
3. Bulala: Mataki na uku shi ne maigida zai horar da mace mai bijirewa ta hanyar duka, ko bugunta da bulala a jikinta. Shi bugun nan za ayi shi ne a daidai lokacin da take cikin bijirewa ga umarnin maigida, kuma za a yi shi ne sama-sama, wato kada ya cika zafi ta yadda har zai nuna alama a jikinta ko ya raunata mata fata, kuma matsakaici wato kada ya yi yawa ta yadda har zai sa ta kasa tashi ko ya kwantar da ita. Za a yi shi ne cikin irin yanayin da za a horar da karamin yaron da ya yi laifi. Kuma a kula sosai kada a buge ta a fuska domin Manzon Allah (SAW) ya yi hani da haka; shi ya sa ya fi dacewa a sa bulala kada a yi dukan nan da hannu, bisa la’akari da karfi jikin namiji da kuma rauni irin na jikin mace.
Sai mako na gaba in sha Allah da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.