Matakan Tinubu 12 na wadata ƙasa da abinci

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sanar da matakan gaggawa 12 da zai ɗauka domin wadatar da al’ummar Najeriya da abinci. Ya ce hakan ya biyo bayan tashin gwauron zabin da farashin kayan abinci ya ke yi. Kakakin shugaban ƙasa Dele Alake ya bayyanawa ƴan jarida jerin matakan a ranar Alhamis. Cire tallafi: Abinci da […]

Matakan Tinubu 12 na wadata ƙasa da abinci

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sanar da matakan gaggawa 12 da zai ɗauka domin wadatar da al’ummar Najeriya da abinci.

Ya ce hakan ya biyo bayan tashin gwauron zabin da farashin kayan abinci ya ke yi.

Kakakin shugaban ƙasa Dele Alake ya bayyanawa ƴan jarida jerin matakan a ranar Alhamis.

Cire tallafi: Abinci da sufuri na cinye albashin ma’aikata a Abuja

Barawon abinci ya kashe manomi a Zariya

  1. Rabawa manoma da magidanta taki da hatsi nan take.
  2. Tabbatar da haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar noma da ma’aikatar albarkatun ruwa domin bunƙasa noman rani da damina.
  3. Kafa Hukumar Amfanin Gona ta Ƙasa domin daidaita farashi da samar da rumbunan adana abinci na ƙasa.
  4. Ƙara samar da tsaro ga gonaki da manoma.
  5. Bunƙasa rawar da Babban Bankin Ƙasa ke takawa wurin samar da jari ga manoma da masu sarrafa amfanin gona.
  6. Inganta ƙasar noma hekta 500,000 domin noman rani da damina.
  7. Bayar da lamuni mai sauƙi ga manoma da makiyaya.
  8. Bunƙasa harkokin sufuri da adana amfanin gona.
  9. Kyautata harkokin cinikin amfanin gona bisa haɗin gwiwa da hukumar kwastan.
  10. Tuttuɗo ƙarin ma’aikata da sababbin ayyuka a fannin noma.
  11. Tabbatar da cewa duk ɗan Najeriya yafi ƙarfin abin da zai ci.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume