Matakan Tinubu na gyara kura-kuran gwamnatocin baya — Minista

A matsalolin da suka hana ƙasar ci gaba akwai hana ƙananan hukumomi ’yanci.

Matakan Tinubu na gyara kura-kuran gwamnatocin baya — Minista

Gwamnatin Tarayya ta ce manufar wasu matakai da Shugaba Bola Tinubu ya ɗauka ita ce gyara wasu kura-kurai da gwamnatocin baya suka tafka domin dawo da tattalin arzikin Najeriya da ƙarfinsa.

Ministan Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Abuja.

Ministan a wata ganawa da ya yi da ’yan jarida ya bayyana yadda ƙasar za ta taƙaita bikin cika shekara 64 da ’yancin kai.

“A ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu, mun kawo wasu muhimman tsare-tsare domin gyara kura-kuran da aka yi a baya, tare da dawo da martabar Nijeriya musamman a ɓangaren tattalin arziki.”

“Duk da matsalolin da aka samu da wahalhalun da ’yan ƙasar suka shiga a sanadiyar matakan, shugaban yana ci gaba da ƙoƙarin inganta tattalin arzikin ƙasar da sanya ta a hanya mai ɗorewa da kowa zai ji daɗi.”

Ministan ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin manyan matsalolin da suka hana ƙasar ci gaba shi ne riƙe maƙwagoron ƙananan hukumomin da gwamnoni suka yi, amma Shugaba Tinubu ya ba su ’yanci domin kai romon dimokuraɗiyya kowane lungu da saƙon ƙasar.

Rikicin Masarautar Kano: Tsagin Aminu Ado Bayero zai ɗaukaka ƙara

Yadda Jimmy Carter ya ceto rayuwata – Obasanjo

Sojoji sun lalata sansanin Bello Turji, sun kuɓutar da mutum 7

Wani mutum ya rasu yayin gyaran rijiya a Kano