Matakan Tsaron Uwargida
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama a gidan mijinta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.Matakan Tsaron Uwargida: A cikin littafinSa mai tsarki, Allah SWT Ya tsara tsaron da ya […]
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama a gidan mijinta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
Matakan Tsaron Uwargida: A cikin littafinSa mai tsarki, Allah SWT Ya tsara tsaron da ya kamata kowace mace Musulma ta kasance a cikinsa a kodayaushe:
“Kuma ka ce ga Mu’uminai mata su runtse daga gannansu kuma su tsare farjojinsu; kuma kada su bayyana kawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta…”
Wannan Aya ta 31 cikin Suratul Nur ta bayyana mana cewa tsarin tsaron mace Musulma ya kunshi matakai guda uku, wadannan su ne:
1. Runtse Gannai
2. Tsare Farji da kuma
3. boye kawa (kwalliya, ado)
Don haka ga bayanin wadannan matakan tsaro daya bayan daya:
1. Runtse Ganin Ido: Daga cikin kafofin hankali guda shida, mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne gani; don haka Allah SWT Ya yi umarni ga Mu’uminai Maza da Mata da su tsare gannansu; domin duk abin da ido ya gani ya fi tasiri ga zuciya sama da jin kunne, jin hanci, jin fatar jiki, jin harshe ko ji na nafsin dan Adam, kamar dai yadda Hausawa ke fadi cewa ‘gani ya kori ji.’ Yawanci daga ganin ido ne har mummunan tunanin sabon Allah ke iya sakuwa cikin zuciya, wanda idan aka bar shi ya zarce, yana iya zama dalilin faruwar ayyukan alfasha. Ganin ido shi ke jaza yin magana tsakanin mace da namijin da ba muharraman juna ba, daga gaisawa sai a shiga tattaunawa da yin fara’a da juna, wanda daga nan ne in Shaidan ya samu nasara sai ya tunkuda su ga aikata aikin alfasha. Kamar yadda Manzon Allah SAW ya sanar mana cewa akwai zinar idanu da zinar kunne da zinar harshe da zinar hannu da zinar kafa da zinar al’aura da kuma zinar zuciya, idan muka lura da kyawu za mu ga cewa zinar ido ke jaza faruwar zinar sauran gabobi shidan. Don haka idan Musulmi ya tsare ganin idonsa daga alfasha, to hakan tsari ne ga sauran kafofin hankalinsa gaba daya daga ayyukan alfasha.
Yadda uwargida za ta tsare ganinta:
Kamar yadda ya gabata a sama, Allah SWT Ya yi umarni ga mu’uminai mata da ‘su runtse daga gannansu,’ runtse gannai a nan na nufin rage kallo a kan mazan da ba muharramai ba, watau mace ta dan sakaya kallonta gare su, ta hanyar yin kasa-kasa da ganinta ko ta hanyar kawar da kanta gefe daya daga inda suke, haka kuma wannan na nufin kada mace ta kura ido ta kalli namijin da ba muharraminta ba gaba dayansa, har ya kai ta yi masa kallon tsab, ta yadda tana ma iya siffanta kamanninsa gaba daya idan aka tambaye ta; lallai wannan irin kallo haramtaccen kallo ne. Don haka uwargida ga irin yadda za ki rika tsare ganin idonki a wurare daban-daban:
• Lokacin fita zuwa unguwa: Uwargida ki sunkuyar kanki kasa kuma ki sa idonki a gabanki, kuma ki mayar da hankalinki gaba daya a kan hanyar da kike bi, kada ki daga kanki kina kallace-kallace, koda kuwa a cikin mota kike, domin mafi yawan abubuwan da za ki gani maza ne wadanda ba muharramanki ba, ko ki ga wani da kika sani, to kada ki tsaya gaisawa da shi a kan hanya ballantana har ki tsaya yin hira da shi, idan ba ki san namiji ba, ko sallama ya yi miki ba lallai sai kin amsa masa ba, ko kuma ki amsa ta hanyar furuci kawai ba lallai sai ya ji kalamanki ba.
• A wajen aiki, ya ’yar uwa mai karamci, sai ki dage wajen yin yaki da kanki ta yadda kodayaushe za ki kasance mai yin kaffa-kaffa don ganin kin tsare ganin idonki. Ki guji yawan hada ido da abokan aikinki maza; komai tsanani ki daure ki rika kawar da idonki in kuna magana da su. Kada ki saki kallonki a kan jikinsu ta yadda za ki yi musu kallon tsab har ki iya kididdige kamaninsu, ko ya kasance hankalinki ya nazarci yanayin shigarsu, domin daga haka ne kila har ki ga wani abun da ya burge ki, ko ya ba ki sha’awa, kuma daga haka ne shaidan zai iya samun kafar saka miki munanan tunane-tunane. Abin kam da wuya, don haka sai kin daure, ki dauki abin a matsayin jihadin nafsi, kuma ki rika hango daraja da kimar da riko da haka zai kawo miki; kuma ki rika tsawata wa kanki da raguwar daraja da sakaci game da wannan umarni na Allah SWT zai kawo miki, wannan zai taimaka ki kara dagewa wajen yin kyakkyawan tsaro ga ganin idonki. Da fatan Allah Ya ba dukkan matan Musumi ikon dagewa ga yin kyakkyawan riko ga wannan umarni na Allah Mai Girma da daukaka, amin.
Sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.