Matakan Tsaron Uwargida (3)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama a gidan mijinta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.3. boye Kwalliya: Allah SWT Ya Umarce mata Musulmi da: “Kada su bayyana kawarsu face […]

Matakan Tsaron Uwargida (3)
Matakan Tsaron Uwargida (3)

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani ga uwargida kan yadda za ta mori zama a gidan mijinta. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya amfanar da masu bukatarsa, amin.
3. boye Kwalliya: Allah SWT Ya Umarce mata Musulmi da: “Kada su bayyana kawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta…”
kawa da ta danganci ’ya mace kashi uku ne: ta yanayin halitta; kawa ta kayan ado da kuma ta dabi’ar halitta. Wajibi ne mace Musulma ta boye duka kashi ukun, kada ta bayyanar da su ga mazan da ba muharramanta ba, face sai abin da ya zama dole ya bayyana daga gare su. Ga bayaninsu daya bayan daya:
•    kawa ta halitta: kawar da ta danganci yanayin halitta ita ce, irin siffar da Allah Ya halitta jikin kowane dan Adam, wadda ita ce wacce ta sha bamban da ta waninsa. Kuma wannan ita ce mafi muhimmancin daga cikin kawa ukun da na ambato a sama; domin irin kyawun da Allah Ya ni’imta  bawanSa da shi ya fi daukar hankalin masu kallo sama da kayan ado ko iya ado.
Mu lura: Mutumin da ba shi da kyawun siffa, komai irin yadda ya kai makura ga sanya kayan ado, ba ya tafiyar da rashin kyawun halittarsa, amma kyakkyawa ko bai sanya komai na daga kayan ado ba, to kyawunsa zai bayyana yana sheki a kodayaushe. Abu mafi kawa a jikin ’ya mace shi ne fuskarta. Ita tafi daukar hankalin mazaje sama da komai, mu lura, komai irin yadda mace ta kai ga kyawun ado da shiga mai kyawu, da fuskarta ake auna darajar kyawunta ba da shigar da ta yi ba.
A bisa wannan dalili ne wasu malaman suke ganin rufe fuska ga macen da ta balaga wajibi ne, domin fuska kawace da ba abin da ya kai ta jan hankalin da namiji. Mace Musulma za ta rufe dukkan kawar halittar jikinta daga ganin idon mazan da ba muharramanta ba, ta hanyar rufe jikinta gaba daya da hijabi mai kauri kuma maras daukar ido yayin da za ta fita daga gida, ko yayin da za ta bayyana gaban mazan da ba muharramanta ba, sai abin da ya zama dole ya bayyana; wadannan su ne hannu da fuska a fahimtar wasu malaman, ko kuma in wani yanayi ya tilasta bayyanuwar wani bangare na jikinta, to wannan babu laifi.
ketare iyakokin Allah ne mace ta rika bayyanar da kawar kirar jikinta na ’ya mace, ta hanyar sanya tufafin da ba su rufe dukkan jikinta ba, sannan ta bayyana a haka gaban mazan da ba muharramanta ba.
•    kawar Kayan Ado: Kayan Ado suna inganta kyawun ’ya mace, su kuma kara mata daukar ido da jan hankali. Yawancin mata iya ado ne ke jan hankalin mazansu zuwa gare su, don haka ne Allah Madaukankin Sarki Ya umarci mata da su boye irin wannan kawa na kayan ado sai ga mazan aurensu kadai, face sai abin da ya zama dole ya bayyana, ta fannin kayan ado kusan ana iya cewa ba wani abu da ya zama dole ya bayyana, domin idan mace Musulma ta sanya hijabinta da kyawu yadda ya dace, hijabin zai boye mata komai na kayan adonta, ko kuma tana iya cire su ta aje lokacin fita, sai ta dawo gida sannan ta mayar.
Kwalliya irin ta fuska ita ma wajibi ne ga mace Musulma ta boye, don haka ga macen da ba ta rufe fuskarta, sai ta kiyaye caba kwalliya a fuskarta yayin da za ta fita waje ko yayin da za ta bayyana gaban mazan da ba muharramanta ba. Haka kuma ana ado da tufafi da kuma yanayin dinkin da aka yi musu da kuma yanayin sanya su a jiki, tufafi mai kwalliya na yanayin sakarsa, dole a boye kwalliyarsa da hijabi marar kwalliya yayin fita, haka yanayin sanya kaya mai jan hankali, kamar daurin dankwali ko zane cikin siga mai jan hankali bai dace ba lokacin fita ko lokacin bayyana gaban mazan da ba Muharramai ba.
•    kawa ta dabi’a: Ita ce kawa da ke gauraye cikin yanayin magana, motsi da sautin muryar wasu daga cikin mutane; wasu matan Allah Ya ni’imta muryarsu da taushi, zaki ko sanyi-sanyi, ta yadda duk namijin da ya saurare su sai ya zaku da ya ga mai wannan muryar; wasu matan kuma Allah Ya ba su baiwar iya tafiya mai jan hankalin da namiji; wasu kuma sun iya yatsina da karairaya; wasu kuma murmushinsu ne mai daukar hankalin, da sauransu. To a nan mace Musulma za ta yi iyakar kokarinta ta boye wanda take iya boyewa daga cikin ire-iren wannan dabi’u, kada ta bayyanar da su sai ga mijinta kawai ko kuma a inda ya zama dole ta bayyanar da su; kada mace ta rika sarrafa muryarta, yanayin motsinta, dariyarta da murmushinta musamman don dai ta ja hankalin mazan da ba muharramanta ba, in ta yi haka tabbas ta tsallaka iyakokin da Allah SWT Ya aza mata.Da fatan Allah Ya ba dukkan matan Musulmi kokarin tsare iyakokin da Allah Ya aza musu game da tsare farji da boye ado.
Sai mako na gaba in sha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.