Matakin ba-sani-ba-sabo ne maganin matsalolin bangaren mai – Shugaban PENGASSAN
Aminiya ta samu tattaunawa da Kwamared Francis O. Johnson, shugaban kungiyar manyan ma’aikatan kamfanonin mai da iskar gas ta Najeriy,a wacce a takaice ake kira PENGASSAN, a wurin taron kaddamar da littafin Tajwidi da aka yi a masallacin kasa da ke Abuja a karshen makon da ya gabata, wanda wani memban kungiyar ya rubuta. Kwamared […]

Aminiya ta samu tattaunawa da Kwamared Francis O. Johnson, shugaban kungiyar manyan ma’aikatan kamfanonin mai da iskar gas ta Najeriy,a wacce a takaice ake kira PENGASSAN, a wurin taron kaddamar da littafin Tajwidi da aka yi a masallacin kasa da ke Abuja a karshen makon da ya gabata, wanda wani memban kungiyar ya rubuta. Kwamared Johnson ya yi bayani dalla-dalla kan matakan da za a dauka a kawo karshen matsalolin da ke addabar bangaren mai da iskar gas a kasar nan. Ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Muna so ka gaya mana nasarorin da ka samu tun lokacin da ka hau kan karagar shugabancin wannan kungiya?
A lokacin da muka karbi ragamar shugabancin wannan kungiyar abin da muka fara shi ne mu tattabar da wanzuwar hadin kai da fahimtar juna a kungiyar PENGASSAN. Mun tabbatar da cewa mun tafi da kowa da kawo babu wanda aka bari a baya. Dalilin da ya sanya muka bayar da muhimmacin a bangaren hadin kai shi ne, muddin babu hadin kai babu yadda za a samu ci gaba a cikin kungiya. Abu na biyu shi ne kare martabar membobinmu. Ba abu ne mai sauki ba a ce an zabo ka daga cikin membobin kungiyar PENGASSAN su kimanin dubu 25. Saboda haka dole ka kare martabarsu da ayyukansu.
Aminiya: Wadanne irin ayyuka kuka gudanar?
Aiki na farko da muka gudanar shi ne na kare martaba da hakkokin membobinmu. Saboda wannan shi ne mafi a’ala. Abu na biyu shi ne kokarin da muka yi na ganin cewa an bunkasa bangaren mai da iskar gas. Wani abu mai muhimmanci shi ne kokarin da muka yi na ganin cewa mun bunkasa hanyoyin kudin shigar kungiyarmu. Abu na gaba shi ne kokarin da muka yi na ganin cewa membobinmu sun sanya kasar Najeriya a gaba fiye da komai. Ta hanyar kishin kasa da gina kasa da ci gabanta. Sannan kuma mun yi kokarin gina wata turba da za ta zama harsashin da sauran shugabanin kungiyar da za su zo nan gaba za su dasa na gina kungiyar.
Aminiya: Wadanne kalubalen kuke fuskanta a halin yanzu?
Babban kalubalen da ke fuskantar kungiyar PENGASSAN da bangaren man fetur da iskar gas da kuma Najeriya baki daya shi ne faduwar farashin mai da fasa bututun mai da satar mai da rashin biyan kudin mai da karya ka’idojin mai da halin da matatun mai suke ciki da sauransu. Ina mai tabbatar maka da cewa idan aka yi maganin wadannan matsaloli to babu shakka kasar nan za ta ci gaba.
Aminiya: Wane kokari kuka yi wajen ganin an yi maganin wadannan matsaloli?
kokarin da muka yi shi ne a lokacin da muka hau kan karagar mulki mun yi kokarin tsara hanyoyin da za a bi wajen magance wadannan matsaloli. Mun rubuta takardar muka mika wa kwamitin da gwamnati ta kafa wanda Alhaji Ahmad Joda ya shugabanta. A takardar da muka rubuta mun bayar da shawarar cewa ya kamata a dauki matakin ba-sani-ba-sabo a bangaren man fetur da iskar gas don ganin cewar duk dokar da aka karya a bangaren an hukunta wadanda suka karya ta. Kuma abin da babban Ministan ayyuka da karamin Ministan ayyuka suka yi a lokacin da batun samar da ayyukan yi ya taso shi ne na kafa kwamiti, kuma abin da kwamitin suka fara yi shi ne na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar. Sun yi taro da kungiyar da sauran kungiyoyi da ke da ruwa da tsaki.
Aminiya: Me ya sa ka ce daukar matakin ba-sani-ba-sabo zai kawo karshen matsalolin da addabar bangaren mai da iskar gas?
Wannan matakin ne mafita, saboda matsalolin sun yi yawa. Akwai matsalar fasa bututun mai da satar danyen mai da faduwar farashin mai da halin kaka-nika-yi da matatun mai suke ciki. Saboda haka dole a duba yadda za a kawo karshen wadannan matsaloli. Ta haka ne duk masu ruwa da tsaki su hada kai su zauna bisa gaskiya da amana su ce daga yanzu wadannan su ne matsalolin da za mu tunkara kuma mu yi maganinsu. Saboda haka wannan ita ce hanya daya tilo da za a kawo karshen dimbin matsalolin da ke addabar bangaren man fatur da iskar gas. Kuma ta haka ne duk ’yan Najeriya za su amince da matakan da aka dauka, kuma ta haka nan ne kasar nan za ta ci gaba.
Aminiya: Shin ka gamsu da matakan da shugaban kasa yake dauka wajen tunkarar kalubalen da bangaren mai yake fuskanta?
Shi ya sa muke cewa in dai ana so a ci gaba dole a dauki matakan da suka dace. Shi ya sa kuma muke cewa dole a hada karfi da karfe don cimma burin da aka sanya a gaba. Gaskiya ne mun gamsu da yadda shugaban kasa yake daukar matakai, mun gamsu cewa akwai Ministan man fetur da shugaban kamfanin NNPC da Janaral Manaja, kuma abin da muke cewa, duk yadda za a yi dole mu hada kai don mu cim ma burin da muka sanya a gaba.