Matakin Babban Bankin Najeriya a kan Dalar Amurka ya dace – ’Yan canji
Wasu daga cikin masu harkokin musayar kudaden kasashen waje da ke Abuja sun yaba wa Babban Bankin Najeriya dangane da wasu matakai da ya dauka game da amfani da Dalar Amurka wadanda ake gani ya shafi harkokinsu. A makon jiya ne Babban Bankin ya lissafa wasu kayayyaki da ake shigowa da su kasar nan wadanda […]
Wasu daga cikin masu harkokin musayar kudaden kasashen waje da ke Abuja sun yaba wa Babban Bankin Najeriya dangane da wasu matakai da ya dauka game da amfani da Dalar Amurka wadanda ake gani ya shafi harkokinsu.
A makon jiya ne Babban Bankin ya lissafa wasu kayayyaki da ake shigowa da su kasar nan wadanda aka rawaito cewa Babban Bankin ba zai kara ba da tallafin canjin Dala ba don shigo da su.
Wannan mataki da bankin ya dauka ya ce ya dauka ne saboda yana ganin hakan zai sa a samu wata hanya da za ta sa a farfado da masana’antun da suka durkushe.
Wannan mataki ya sa Dala ta cira sama a makon farko da fitar da dokar, sai dai a ranar Litinin din da ta gabata da bankuna suka fara kin karbar ajiyar Dala, sai darajar Naira ta fara farfadowa.
Duk da cewa wasu suna ganin cewa wannan sabon tsari ya yi tsauri, masu harkokin canji suna ganin hakan yana da alfanu don zai hana tashin gwauron zabo da Dalar Amurka ke yi.
Malam Umar Garkuwa, wani fitaccen dan canji a kasuwar canji da ke Zone 4 a Abuja, ya ce a nasa ganin wannan tsari ne zai kawo ci gaba ga tattalin arzikin kasar nan.
“A yanzu ta kai mutane da yawa sai su rika sayen Dala suna boyewa a gidajensu ko kuma su kai bankuna su ajiye a cikin asusunsu. A wasu wuraren ma idan za ka yi cinikayya a gida sai a ce wai sai dai ka biya da Dalar,” inji Garkuwa.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa a wasu jihohi, musamman a Birnin Tarayya, Abuja akwai makarantun boko wadanda ba na gwamnati ba da ba su karbar Naira sai dai iyaye su biya kudin makarantar ’ya’yansu da Dalar Amurka.
A halin yanzu bude asusun Dalar Amurka a Najeriya yana nema ya zama ruwan dare.
Sai dai ga alama cire wannan tallafi na canjin Dala da Babban Bankin Najeriya ya yi, ya dan girgiza farashin kayayyakin bukatun yau da kullum musamman shinkafa, wadda farashinta ya haura sama.