Matakin dangote kan noman shinkafa ya yi

Matakin dangote kan noman shinkafa ya yi Editan Aminiya ka ba ni dama in nuna farin cikina game da matakin da hamshakin dan kasuwa, mai kafa masana’antu, Alhaji Aliko dangote ya dauka a noman shinkafa. Hakika mu talakawan Najeriya mun yi farin ciki da matakin da Aliko dangote ya dauka na habaka noman shinkafa gami […]

Matakin dangote kan noman shinkafa ya yi
Matakin dangote kan noman shinkafa ya yi

Matakin dangote kan noman shinkafa ya yi

Editan Aminiya ka ba ni dama in nuna farin cikina game da matakin da hamshakin dan kasuwa, mai kafa masana’antu, Alhaji Aliko dangote ya dauka a noman shinkafa. Hakika mu talakawan Najeriya mun yi farin ciki da matakin da Aliko dangote ya dauka na habaka noman shinkafa gami da sarrafata a Jihar Jigawa, wanda hakan ba karamin ci gaba ba ne, kuma hakan zai yi matukar taimaka wa tattalin arzikin Najeriya ta hanyoyi biyu a takaice. Na farko zai taimaka wa tattalin arzikin Najeriya ta wajen samun karin kudin shiga gami da rage dogaro ga kasashen waje, musammam wajen shigowa da shinkafa kasar nan. Na biyu zai taimaka wa tattalin arzikin Najeriya ta wajen rage masu zaman banza, ganin yarda zaman banza ba karamin nakasu ba ne ga kowane tattalin arziki. Daga karshe ina kira ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da ta bai wa wannan shirin na Aliko dangote goyon baya dari bisa dari, domin ceto tattalin arzikin Najeriya daga halin da yake ciki a yanzu na tabarbarewa.  
Daga Salim Abubakar Imam Jingir dalibi a Tsangayar Nazarin Tattalin arziki a Jami’ar Musulunci da ke Katsina, kuma Shugaban kungiyar Muryar Talaka reshen Jihar Filato 08067922200. [email protected]

Mun yi rashin wakili a Funtuwa    
Tun bayan rasa wakilinmu a majalisar wakilai, mai wakiltar Funtua/dandume, watau Hon. Dokta  Mansur Abdulkadir Funtuwa,har yanzu ba mu san inda aka dosa ba, a zamanin jagorancin Dokta Mansur mun samu sauyi mai ma’ana, ya biya wa dalibai kudin jarabawar WAEC da NECO, ruwan Bore-hole ko wane sako. Hakika mun yi rashin wakili adali.
Daga Mainasara Nasarawa Funtua. 08034208356

Amsa ga Abdu Ba Ka Noma                      
Assalamu. Ma’aikatan Aminiya da fatan duk kuna cikin koshin lafiya, ma’aikatan wannan jarida mai’albarka Aminiya, da Allah ina so a isar min da amsar tambayar nan ta “Aminu Abdu Baka noma” da ya yi akan talakan Najeriya da  tsarin mulkin Shugaba Buhari (PMB). Amsa ta farko (1) idan gyara muke so dole sai mun jure, su ma masu gyaran sai sun jure.   (2) Hana hada-hadar Dalar Amurka, ga ’yan kasuwa? Dole sai da darajar kudi kasa take samun ci gaba. (3) Ka ce talakawa mun kosa? indai mun jure za mu mure.
Daga danladi Abdulmumini Baka Hutun noma, Fulata, karamar Hukumar Maigatari, Jihar Jigawa.

Kuka ga Sarkin Daura
Zuwa ga Edita bayan gaisuwa mai yawa da fatan alkhairi ayau inaso abani dama domin inyi kuka ga mai martaba Sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar. Kukan kuwa, shi ne, Maimartaba muna so  ka kafa wa direbobi dokar hana gudu tsakanin GRA da Gurjiya. Domin Allah ya kara maka lafiya na san cewa, kafini  sanin cewa, tun daga GRA zuwa Gurjiya duk cikin gari ne, amma irin yadda drebobi suke yin gudu a wannan tsakani wallahi sai ka yi zaton Legas mutum zai tafi, saboda yawan hadarin da ake yi a wannan tsakani, abun babu kyau. Don haka mun yi imanin kai kadai za ka iya yi mana  maganin abun.
Daga Hadi Tsohon Sarki Daura 08148442241 08085127726

Zaben Jamhuriyar Nijar  
Assalamu alaikum Edita namu mai aikin a kan gaskiya a yau ina so ka ba ni dama in taya al’ummar kasar Nijar murnar kammala zabe lami lafiya wannan babban abin farin ciki ne gare su. Muna kara yi musu addu’a da fatan Allah ya ba su shugaba nagari mai tausayin a’ummar su ba mai tausayin aljihunsa ba.
Daga Umar Idirisa Bappa Askira Jihar Barno 08062350519

Yabon Gwani Ya Zama Dole
Duba da irin damar da kundin tsarin mulki na kasa ya bai wa kowane dan kasa ta yana iya tsokaci a kan al’amurran duniya, ba tare da katsalandan ba. Don haka, ina jinjina wa Sanata Kabiru Marafa mai wakiltar yankin Zamfara ta Tsakiya, saboda kokarinsà na ganin bayan matsalar satar shanu a jiharmu ta Zamfara, matsalar da ta dade tana ci mana tuwo-a-kwarya.Ta hanyar kai wa wadanda ibtila’in ya fadawa ziyarar jaje, tare da kai musu kayan tallafi. Haka kuma,ina kira ga sauran takwarorinsa masu wakiltar yankunan Zamfara ta Yamma da ta Arewa da su yi koyi da shi, ta fuskar kawo wa wadanda abin ya shafa tallafin gaggawa.  Da fatan Allah ya kawo mana karshen wannan matsala ta satar shanu a duniya baki daya.
Daga Nura Sule Jangebe jihar Zamfara Najeriya.08139326016 dan kungiyar Muryar Talaka.
Fatan alheri ga al’ummar Nijar…
Assalamu alaikum, Aminiya mai farin jini Hausa. Ku bani dama na mika sakon fatan alkhairi ga al’ummar kasar Jamhuriyar Nijar, sakamakon zaben da su kayi cikin tsanaki da lumana ba tare da tada jijiyoyin wuya ba. Hakika al’ummar Nijar kun baiwa mara da kunya kwarai da gaske, shawararmu agareku ita ce ku kasa ku tsare kuri’unku har sai hukumar zaben Niyar wato (Ceni) ta yi adalci ya yin bayyana wa duniya sahihin abin da kuka zaba domin gudun abin da zai biyo baya. A karshe muna kira ga al’ummar Nijar da su ci gaba da kasance wa tsintsiya daya al’umma daya, su kuma ‘yan takarar duk wadda ya sha kayi to ya runguni kaddara, wadda kuma ya samu nasara kuma ya rungumi kowa da kowa a matsayin ‘yan kasa kaya al’umma daya, ba tare da nuna fifiko a tsakaninsu ba. Adamu Aliyu Ngulde, Da Isma’il Ibrahim El-Barnawi,
Daga kungiyar Muryar Talaka Reshin Jihar Borno. 09032135939. [email protected]
Kira ga shugaba Buhari
Salam. Don Allah kamfanin jarida ku isar da sakona a gaya wa shugaban kasa Muhammad Buhari ya kara kaimi abisa doka da oda, don gudun cin mutunci a Najeriya.
Daga Tasiu Usman, Abuja  07066752777.
Taya murna ga Sherrif
Assalamu alaikum. Aminiya kotun talaka  Edita.  Don Allah ina so ka ba ni dama  in mika sakon taya murna ga tsohon Gwamnan Jihar Barno, bisa matsayin da Allah ya ba shi na Shugaban jam’iyyar P.D.P na kasa  da fatan Allah ya yi jagora.  
Daga Jamilu Gambo Takai.08166835313 Jinjina ga Gwamna Badaru
Addu’a  ga Aminiya  
Edita ni mai karanta  jaridar Aminiya ne, mai farin jini. Ubangiji Allah ya kare ku daga masharranta amin.
Daga Mista Molta Dickautal  Maiduguri.

Kira ga Gwamna Kano
Salam. Don Allah a yi kira ga gwamna kano ayi wa malaman primary promotion allah yabada ikon ye amee muna godiya jarida Aminiya daya cikin dari muna godiya.
Daga Nazifi Hassan Gwarzo, Jihar Kano 08066926647.

Jinjina  ga Gwamna Badaru
Editan Aminiya ina yi wa Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru jinjina da ya duba cancanta da ganin muhimmancin kowane dan Jihar Jigawa, musamman ganin yadda ya bai wa Malam Habibu Sani babura shugabancin kwmaitin kula da kwalejin koyon shari’ar Musulunci da ke Ringim. Allah Ya sa ka gaji Baba Buhari, wajen shugabanci.
Daga Alhaji Lawal Abubakar baure 07060792797.