Matakin gwamnati na janye kara kan iyalan Abacha

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana janye karar da ta shigar kan iyalan marigayi Janar Sani Abacha, a kokarinta na karbo kudin da ake zargin marigayin ya sace, ya boye a kasashen ketare lokacin da yake Shugaban Mulkin Sojan Najeriya. Matakin ya fito karara ne bayan bayyana cewa ta janye dukannin tuhumar da […]

Matakin gwamnati na janye kara kan iyalan Abacha
Matakin gwamnati na janye kara kan iyalan Abacha

A kwanakin baya ne Gwamnatin Tarayya ta bayyana janye karar da ta shigar kan iyalan marigayi Janar Sani Abacha, a kokarinta na karbo kudin da ake zargin marigayin ya sace, ya boye a kasashen ketare lokacin da yake Shugaban Mulkin Sojan Najeriya. Matakin ya fito karara ne bayan bayyana cewa ta janye dukannin tuhumar da take wa babban dan tsohon shugaban, Muhammad Abacha. An danganta tuhumar tasa da halarta kudin haram da suka kai Naira biliyan 446 da miliyan 300 wadanda aka sace daga baitul-malin gwamnati a tsakanin shekarar 1995 zuwa 1998.
Kodayake takardar tuhumar ta bayyana cewa ana zargin Muhammad ne da taimaka wa mahaifinsa wajen yin sama da fadi da kudin da suka kai kimanin Dala biliyan 3 zuwa 5, wadanda aka boye a asusun bankuna da dama a fadin duniya. Amma a wani mataki mai kama da kunbiya-kunbiya, Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a Mista Muhammad Adoke ya shaidawa Babbar Kotun Tarayyar da ke sauraron karar cewa ya janye duka tuhumar da ake wa Muhammad Abacha.
Kalaman Allah-wadai daga dimbin jama’a da kuma kasashen duniya ne suka tilasta wa Mista Adoke yin bayani dangane da matakin. Inda ofishinsa ya fitar da wata sanarwa da ke cewa gwamnati ta dauki matakin ne domin dacewar yin hakan, amma ba don kare Abacha daga tuhuma ba. Mista Adoke ya bayyana cewa kafin daukar matakin, Gwamnatin Shugaba Jonathan ta tuntubi masana da wasu kungiyoyin kasashen ketare da kuma abokan hulda da dama domin neman shawararsu.
Ministan Shari’ar ya kuma ce janye tuhumar zai taimaka wajen dawo wa da kasar nan Dala miliyan 380 daga kasar Ludembourg da wasu Dala miliyan 550 wadanda Ma’aikatar Shari’ar kasar Amurka ta karbe.
kungiyar yaki da cin-hanci da karbar rashawa ta Transperency International (TI) ta yi Allah-wadai da matakin, inda ta ce: “Bai kamata a bari ana sace dukiyar al’umma ba, ba tare da hukunta wadanda suka yi hakan ba, wannan na aika mummunar sako ga masu rike da madafun iko. Zai yi kyau idan da an ci gaba da sauraran karar bisa la’akari da yadda gwamnati ta kasa ba da gamsasshun hujjojin da suka sa ta janye karar.” Inji kungiyar.
Mista Adoke ya ce duk wani wanda ke tababa cewa Abacha da iyalansa sun tsira ba tare da rasa komai ba a shari’ance, ba wanda ke kaunar gaskiya ba ne. Kodayake kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin-hanci ta gabatar da kokenta a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke jihar Legas tana kalubalentar matakin Gwamnatin Tarayyar.
Har ila yau matakin janye karar na nuni da gazawar gwamnati wajen yaki da laifukan da suka shafi cin-hanci da karbar rashawa. Kamar yadda al’amura suke a yanzu, gwamnati na kokarin samun goyon bayan jama’a ne a yakin da ta ce tana yi da cin-hanci. A lokaci guda kuma ga matsalar dimbin kararraki da ke dakon hukunci. Bugu da kari, matakin janye karar ya kara tabbatar da batun da ake cewa za a iya yafe wa mutum kowane irin laifi ya yi a kasar nan, ta hanyar sa shi ya dawo da abun da ya sata ko wani abu daga ciki, daga bisani kuma a yafe masa laifinsa. Wannan ya sa ake wa gwamnatin kallon ta gaza kuma hakan yake shafar kimarta a yakin da take da cin-hanci da karbar rashawa.
Mista Adoke ya ce tsohuwar gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo ce ta fara shirye-shiryen sulhuntawa da iyalan Abacha a lokacin da ake kokarin karbo kudin da ake zargin marigayin ya sace, amma sai kamfanonin da suke ajiye kudin suka ki. Wannan ya sa aka kai batun gaban kotu.  
Hakazalika, matakin janye karar na zuwa ne a lokacin da wasu suke wa Muhammad Abacha kallon wani wanda ke kyasawa da uwar Jam’iyyar PDP da kuma batun da ake cewa shi ne jam’iyyar take kokarin tsayarwa a matsayin dan takarar gwamna a zaben shekarar 2015. Idan hakan ya tabbata, kamar ka yi kirari ne kuma ka daba wa cikinka wuka. Yin Allah-wadai da matakin janye karar abu ne da ya kamata.