Matakin Gwamnatin Edo na tsaftace bara zai inganta al’amura – Badamasi Saleh
A cikin makon makon da ya gabata ne Gwamnatin Jihar Edo ta sa aka kama sarkin makafi na Benin, Alhaji Ahmadu Gwaram tare da wadansu mukarrabansa. Wannan matakin ya biyo bayan wani bincike da ta yi ne inda ta gano cewa a cikin mabaratan akwai mata wadanda ba batun barar kadai suka sanya a gaba […]
A cikin makon makon da ya gabata ne Gwamnatin Jihar Edo ta sa aka kama sarkin makafi na Benin, Alhaji Ahmadu Gwaram tare da wadansu mukarrabansa. Wannan matakin ya biyo bayan wani bincike da ta yi ne inda ta gano cewa a cikin mabaratan akwai mata wadanda ba batun barar kadai suka sanya a gaba ba, ana zarginsu da saba wa dokar addini da al’ada kuma irinsu ne suke debo ’ya’yan mutane daga Arewa su kawo su zuba su a kan manyan tituna na cikin garin Benin.
Alhaji Badamasi Saleh ya bayyana cewa: “Kafin hakan da gwamnatin ta yi hakan, ta kira mu ta sanar da mu da shugabanni , muka ba da shawarwari irin abin da muke ganin ya dace a yi, domin a cewar ita gwamnatin, tana so ne ta tsaftace jiha don haka kada a yi wa gwamnatin jihar mummunar fahimta, musamman a bangaren karatun yara wadanda su baragurbin matan suke kange su daga samun ilimi na zamani da na addini. Don haka shawararmu da kiran da za mu yi wa gwamnatocin Arewa ita ce, su yi wa Allah su tanadar wa wadannan mabaratan wuraren kare mutunci da masauki.”
Shi kuwa Sarki samari na kungiyar makafi na Benin, Yahaya Abdullahi cewa ya yi,“Ba wai muna jayayya da gwamnatin ba ne, sai dai muna rokon ita gwamnatin ta tausaya mana domin ba mu da wata sana’ar da za mu samu abinci mu da na iyalanmu, duk da cewa mun san akwai baragurbi a cikinmu kamar yadda muke jin ake zargin wasu mata masu zuwa daga Arewa suna sharholiya a cikin garin Benin.”
Ya ci gaba da bayanin cewa: “Sarkin makafi ya yi iyakacin kokarin ganin hakan da iran wadannan baragurbin matan suke yi a Benin bai ci gaba da dorewa ba sai dai hakarsa ba ta cin ma ruwa ba, don haka abin da gwanmatin jihar ta yi mu kungiyarmu makafi muna biyayya gare ta, domin ba mu da karfi da za mu yi jayayya da gwamnati.”
Shi kuwa Sarkin Makafi Alhaji Ahmadu Gwaram da yake tsare, ya shaida wa Aminiya ta waya cewa ana tsare da su a wani wuri da ake tsare kangararrun yara kusan mako guda. “An yi mana dirar mikiya a wurin da muke bara a kofar gida da muke haya a Mission Road cikin garin Benin. Wannan kamun da suka yi mana ya ba mu mamaki, domin abin ya zo mana ba-zata amma duk da haka ba za mu dora wa gwamnati laifi ba.” Inji shi
Ya ce: “Zargin da ake yi wa wasu matan ai ba matan makafinmu ba ne, wasu ne daban wadanda ba a cikinmu suke ba, don haka ina kiran irin wadannan mata baragurbi su yi wa Allah su natsu, su bi doka da oda, su daina zubar mana da mutunci.”
Ya kara da cewa wadanda suke tsare a hannun hukuma sun hada da mutane 24, a ciki akwai makafi goma sha biyu har da shi sarkin da matansu hudu da ’yan jagoransu guda takwas da sauran wasu yara wadanda ya ce bai san inda aka kai su aka tsare ba.
Wani kuma na hannun daman sarkin makafin, Waziri Dogo ya ce suna rokon a sassauta masu wannan dokar kuma gwamnatin ta taimaka ta sake masu mutanensu da suke tsare. “Za mu ci gaba da kiyaye doka da oda, za mu ba gwamnatin hadin kai a kan shirinta na tantancewa da tsaftace komai a jihar.” Inji shi.
Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin ’yan Arewa mazauna jihar, Alhaji Sahabi Aliyu Umar (J.P) a cikin bayaninsa ya ce: “Abin da na fahimta a cikin wannan yunkuri na gwamnati na wannan karon shi ne tantance mabarata zaunannu da baki masu shigowa suna bata wa wadanda suka same su a jihar shekaru da dama, ba su da wata fitina, musamman makafi. Kuma akwai abin lura a nan a cikin irin wadannan mabaratan akwai bara gurbin mata masu fasadi kuma bugu da kari suna kwaso yara kanana wadanda ya kamata su bar su a gaban iyayensu, su samu ilimi amma sun bi sun kange su suna gurbata tarbiyyarsu; wanda hakan ba zai haifar wa kasar nan alheri ba a nan gaba.
Wakilin Aminiya ya yi iyakacin kokari domin samun haske ko karin bayani a kan wannan yunkuri na gwamnatin jihar amma hakar ba ta cin ma ruwa ba domin ya kira wayar kwamishina mai kula da hukumar al’amuran mata da yara ta jihar, Madam Blessing Maigida har sau uku tana kara ba ta daga ba kuma ya rubuta mata sakon tes amma babu amsa. Sai dai wata majiya mai tushe ta kusa da offishin hukumar ta tabbatar da cewa akwai makafi maza da matansu da wasu yara da suke tsare a hannun hukumar a ciki har da Alhaji Ahmadu Gwaram Sarkin makafi na Benin.