Matakin zama marubuci

Rubutu na da ma’ana daban daban ga mutane mabambanta, inda wani kan yi rubutu don dauke kewa, ko don biyan wasu bukatu ba don kudi ba ko neman suna. kwarewa kan sa wani lokacin za a iya neman ka don ka rubuta littafi kan wani bayani daban da fahimtarka.Kowa zai iya zama marubuci! Duk da […]

Matakin zama marubuci
Matakin zama marubuci

Rubutu na da ma’ana daban daban ga mutane mabambanta, inda wani kan yi rubutu don dauke kewa, ko don biyan wasu bukatu ba don kudi ba ko neman suna. kwarewa kan sa wani lokacin za a iya neman ka don ka rubuta littafi kan wani bayani daban da fahimtarka.
Kowa zai iya zama marubuci! Duk da cewa rubutu baiwa ce, wasu kan fara samun fahimtar rubuta littafi da zama mawallafa tun suna sauraren tatsuniyoyi. Sannan wasu a dalilin yawan karance-karance, wasu kuma kan rubuta littafi a dalilin neman kudi ko bada tarihin idan mutum ya sami tsawon rai, wani lokacin za a neme ka don a sami wani bayani kan abin da ya faru a baya!
Yawan karance-karance ga sabon marubuci, marubuci da marubta fa’ida ne! domin duk wanda ya fi ka karatu ya fi sani, kuma duk takardar da ka karanta sai ka karu daga wani abu a cikinta! Yayin da yawan karance-karancen ke sa mutum ya zama mai yawan rubuce-rubuce. Shi kansa yawan rubuce-rubuce akan fannoni daban-daban ka sa marubuta su zama gwamnati, ta yadda su zasu karkata tunanin al’umma tare da ba matasa saitin kuma su dauki hoton adabin da zai zama tarihin mutanen. Su sami riba su sha romonsu!
Wasu dalibai kuwa, tun a makaranta su ne a gaba wajen muhawara, musamman a darasin harsunan da suka hada da Hausa da Larabci da Turanci, hakan zai ba su miza akan sa’aninsu ‘yan aji daya wajen rubuta littafi, balle sun hada abin da fassara. Kuma kamar kowane dan fim din da ya iya kowane  taka matakin wasa (role), walau ya fito a matsayin mutumin kirki, mai ban dariya, maketaci, malami da sauransu, sai ya zama tauraro! Haka ma marubuta, duk wanda ya yi bajintar jan hankalin yara, manya da tsaffi sai ya zama gwani.
Rubuta littafi kan fara daga abu kadan ko karamin rubutu a mayar da shi labarin da zai ja hankalin kowa da kowa! Ka sami sunan mutanen da za su shigo cikin garin da ka gina a tunaninka. Sannan bayan ka gama hada labarinka ka yi aiki da ka’idojin rubutu domin sau da yawa littafin kan fadi a gasa domin ba a kiyaye ka’idoji ba.
Sannan yana da kyau sabon marubucin ya nemi shawara wajen tsaffin marubuta, ta haka ne rubutun zai zo da sauki tare da samun damar fitar da bakandamiya a tashin farko. Yana da kyau ka ba wani ya duba ma kurakurenka, kuma ka yadda ka gyara, karka yi gardama da wanda ya fika horo, ka nemi shawara kuma ka dauki abin da ka san zai amfane ka, domin kar ka tafka kuskuren da zai sa ka nadama har abada!
Littafin farko yana da muhimmanci ga kowane marubuci, domin ya kan zama jigon duk rubuce-rubucen da marubucin zai yi a rayuwarsa, duk da cewa wasu marubtan kan sauya salo, ko sunan da suke amfani da shi a wajen rubuce-rubucensu don jan hankalin makaranta.
Yadda ake buga littafi da farko ka tara kudi ka dauki nauyin bugawa da kanka wanda hakan shi ne abin daya fi faruwa ga sabbin marubuta. Ko ka rubuta ka ba wani ko wasu manyan mutane ko kungioyoyin marubuta ko shi kan shi amwallafin naka kan auna idan da riba sai ya buga! Idan littafi ya yi kyau, akwai yiwuwar a sace fasahar, a buga, a yada shi ba tare da izinin marubucin ba a rubuce, a nan ma sai hakuri domin mabarnatanmu sun yi nisa, ko don ba mu da basirar kama su? A haka dai ake taka matakin zdama marubuta, don amfanin kai d ana al’umma.
daukar nauyin sayarwa ma wani kalubale ne, musamman idan baka da shago, domin ana shan jeka ka dawo, wani lokaci ka ga ba littattafan kuma ba kudi, sai ka yi hakuri, ko ka sadaukar da kudin domin littafin ya fito!
Za a iya samun Daure akan lamba kamar haka: 07035986444 Muryar Talaka.

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50

Jami’an Sibil Difens sun kashe mayaƙan Boko Haram 50