Matan Borno za su shiga aikin nemo ’yan matan da aka sace

Wasu mata a Jihar Borno sun bayyana niyyarsu ta zuwa dajin Sambisa domin aikin nemo ’yan matan da aka sace daga Makarantar Sakandaren Gwamnati (GGSS) da ke Chibok kusan mako biyu da suka gabata.Matan sanye da bakaken sutura sun yi kuka kan lamarin inda suka yi kira ga kungiyar Boko Haram su sako ’yan matan, […]

Matan Borno za su shiga aikin nemo ’yan matan da aka sace

Wasu mata a Jihar Borno sun bayyana niyyarsu ta zuwa dajin Sambisa domin aikin nemo ’yan matan da aka sace daga Makarantar Sakandaren Gwamnati (GGSS) da ke Chibok kusan mako biyu da suka gabata.
Matan sanye da bakaken sutura sun yi kuka kan lamarin inda suka yi kira ga kungiyar Boko Haram su sako ’yan matan, inda suka kara da cewa, kama su cin zarafin dan Adam kuma zai yi nakasu ga samar da ilimin yara mata da ci gaban jihar da kuma kasa baki daya.
Farfesa Hauwa Biu wadda ta yi magana a madadin matan a taron manema labarai a Maiduguri cikin kuka ta ce, “Mun shirya mu tafi dajin domin nemo su idan za mu samu wanda zai jagorance mu, wadannan ’yan mata barrantattu ne da bai kamata a cutar da su ba.”
Ta kara da cewa: “Kama ’yan mata marasa laifin tsaye ko na zaune tauye musu hakki ne, kuma laifin cin zarafin dan Adam ne a karkashin dokokin kasashen duniya. Mata a Jihar Borno suna matukar Allah wadai da wannan aiki na cin zarafi, domin kai hari ga makarantu yana hana yara samun damarsu na samun ilimi cikin kwanciyar hankali, kuma hakan yana jefa makomarsu a cikin hadari.”
Farfesa Hauwa ta ce: “Muna kuma Allah wadai da dukan hare-haren bama-bamai da kashe-kashen da ake aiwatarwa a sassan kasar nan, kuma muna mika ta’ziyya ga daukacin iyalan wadanda suka rasa rayukansu a wadannan hare-hare marasa dadi. Kuma a yayin da muke kira ga ’ya’yan kungiyar da su yi wa Allah su saki dukkan wadanda suke tsare da su cikin gaggawa ba tare da cutar da sub a, kuma yana da kyau su ajiye makamansu su rungumi tattaunawa, muna tabbatar musu da goyon baya na iyay wajen sake karbarsu a cikin jama’a idan bukatar haka ta taso.”   
Ta yaba wa kokarin Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Borno wajen magance hare-hare, sai dai ta yi kiran a kara samar da tsaro a dukan makarantu ta yadda yara za su rika samun ilimi a yanayi na kwanciyar hankali.
Wakilinmu ya ruwaito cewa mata daga kungiyoyin da ba na gwamnati ba da dama ne suka hadu domin yin kiran a sako ’yan matan ’yan makaranta.