Matan da ke auren ’yan Najeriya a Afirka ta Kudu sun kafa kungiya

Matan da ke auren ’yan Najeriya a Afirka ta Kudu sun kafa kungiyar matan auren Najeriya ta UNW, wato Hadaddiyar kungiyar Matan da ke auren ’Yan Najeriya.Nuna gazawa wajen tantance launin takardar  shaidar aure, tsakanin Thelma Okoro da Kenneth Sunday Okoro, ya kusa zama sanadiyyar raba auren dan Najeriya da matarsa ’yar Afirka ta Kudu. […]

Matan da ke auren ’yan Najeriya a Afirka ta Kudu sun kafa kungiya

Matan da ke auren ’yan Najeriya a Afirka ta Kudu sun kafa kungiyar matan auren Najeriya ta UNW, wato Hadaddiyar kungiyar Matan da ke auren ’Yan Najeriya.Nuna gazawa wajen tantance launin takardar  shaidar aure, tsakanin Thelma Okoro da Kenneth Sunday Okoro, ya kusa zama sanadiyyar raba auren dan Najeriya da matarsa ’yar Afirka ta Kudu. Thelma Okoro (wadda aka fi sani da Dee), ’yar Afirka ta Kudu ce da mijinta Kenneth Sunday Okoro, sun je ofishin harkokin cikin gida ta kasar Afirka ta Kudu don tattaunawa da su kan auren da suka yi.
Kasancewar mijin bako dan kasar waje, dole ne hukumomi su bi kadin auren don tantancewa kan ko an yi shi ne , ta hanyar biyan matar wasu kudi, ita kuma ta taimaka wa mijin ya samu zama dan kasa, saboda auren ’yar kasa da ya yi. An na da su cikin nasara, amma da aka tambaye su launin takardar shaidar aurensu sai “Mijina ya ce ja ce; ni kuwa na ce ta yi launin tsatsa,” a cewar Thelma, inda ta ce: “akwai yiwuwar hakan ta kasance. Saboda maza na fama da makantar bambance launi, amma duk da haka jami’an tsaro suka doge a kan wannan matsalar.”
dimbin matsalolin kyara dam azaje ’yan Najeriya da ke auren matan Afirka ta Kudu ta sanya matan suka kafa kungiyarsu, don kalubalantar wadanda ke kokarin cutar da su saboda sun auri ’yan Najeriya. Wannan kungiya dai an yi mata lakabi da UNW (United Nigerian Wibes – wato Hadaddiyar kungiyar matan da ke auren ’yan Najeriya). kasar Afirka ta Kudu da Najeriya, kasashe da ke da huldar cinikayya a tsakaninsu. Kuma a Najeriya ba a nuna wa ’yan kasuwar Afirka ta Kudu kyara, tamkar yadda ake nuna wa ’yan Najeriya a Afirka ta Kudun.
A bara dai wannan kungiya ta matan auren Najeriya, har barazanar yin zanga-zanga ta yi don kare muradin mazajensu a wannan kasa. Jaridar Mail & Guardian ta Afirka ta Kudu ruwaito cikakken labarin, kan yadda matan ke nuna kauna da soyayya ga mazajensu ’yan Najeriya, har ta kai ga kafa kungiyar don tunkarar duk wani kalulabe da suke fuskanta su da mazajensu a kasar.