Matan da suka karairaya yaro sun gurfana a gaban kotu

A shekaranjiya Laraba ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gurfanar da matan nan da ake zargi da karairaya dan kishiyarsu dan wata 20 mai suna Musa Murtala a gaban Kotun Majistare ta 10 da ke Nomansland a birnin Kano.dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Shu’aibu Musa ya shaida wa kotun cewa ana zargin […]

Matan da suka karairaya yaro sun gurfana a gaban kotu
Matan da suka karairaya yaro sun gurfana a gaban kotu

A shekaranjiya Laraba ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta gurfanar da matan nan da ake zargi da karairaya dan kishiyarsu dan wata 20 mai suna Musa Murtala a gaban Kotun Majistare ta 10 da ke Nomansland a birnin Kano.
dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Shu’aibu Musa ya shaida wa kotun cewa ana zargin matan ne da hadin kai wajen yunkurin kashe yaron.
Shi ma da yake fassara kunshin tuhumar Magatakardar Kotun, Sharif Abdulmumini ya kara da cewa ana zargin kishiyoyin mahaifiyar yaron wato Zainab Murtala da Hafsatu Murtala da karairaya hannuwa da kafafun yaron baya ga ji masa raunuka a baki da kunne da ido da kuma mazakutarsa.
Sai dai da aka waiwayi matan sun musanta laifin da ake zarginsu da shi inda suka ce haka kawai yaron yana kwance salin alin sai aka ga ya tashi da wadannan raunuka a jikinsa inda suka danganta hakan ga Allah.
Alkalin kotun Mai shari’a Maryam Ahmad Sabo ta dage shari’ar zuwa ranar 28 ga Yuni, kuma ta bayar da umarnin a tsare matan a kurkuku. Kuma kotun ta bayar da umarnin ’yan sanda su tuhumi mahaifin yaron.
A shekaranjiya Laraba da safe an yi ta yada jita-jita ta kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa yaron ya rasu. Sai dai da Aminiya ta ziyarci Asibitin Murtala ta iske yaron yana ta wasa da kafafunsa da suke sakale sakamakon dorin karayar da aka yi masa a asibitin.
Mahaifiyarsa Bikisu Usama ta ce Musa yana samun sauki sosai kuma yana samun kulawa daga likitoci da kuma jama’ar gari.
Malama Bilkisu ta yi korafi kan yadda kakan yaron ya zo har asibitin yake neman ta ba shi yayar Musa wato A’isha da gwamnatin Kano ta damka ta a hannunta, inda ta ce sai da ma’aikatan asibiti suka shiga tsakani sannan ya bar asibitin.

Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 214 a Najeriya — NCDC

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe