Matan gwamnoni sun ba matan da aka yi wa fyade a Zamfara tallafi
Kungiyar Matan Gwamnonin Najeriya ta tallafa wa wasu mata biyu da aka yi wa fyade a Zamfara da kudade. Kungiyar ta ce tallafin ga matan da abun ya ritsa da su a Jihar ta Zamfara ne da nufin habaka tattalin arzikinsu. Yadda dubun mai yi wa yara maza fyade ta cika An cafke dillalin makaman […]
Kungiyar Matan Gwamnonin Najeriya ta tallafa wa wasu mata biyu da aka yi wa fyade a Zamfara da kudade.
Kungiyar ta ce tallafin ga matan da abun ya ritsa da su a Jihar ta Zamfara ne da nufin habaka tattalin arzikinsu.
- Yadda dubun mai yi wa yara maza fyade ta cika
- An cafke dillalin makaman ’yan bindiga a Zamfara
- Yau ce Ranar Barci ta Duniya
Sanarwar da sakatariyar yada labaran matar gwamnan Zamfara, Zainab Shu’aibu ta fitar ta ce gudunmawar na daga cikin kokarin matan gwamnonin na yakar tauye hakkin mata da kuma rigingimun cikin gida.
An ba kowacce daga matan da tsautsayin ya ritsa da su tsabar kudi Naira dubu dari.
Kwamishiniyar mata ta Jihar Zamfara, Zainab Lawal Gumi wadda ta wakilci gwamnan Jihar, Aisha Bello Matawalle ce mika kudaden a madadin Kungiyar Matan Gwamnonin.