Matan Gwamnonin Arewa sun tallafa wa matan jami’an tsaro da aka kashe a Nasarawa
Matan Gwamnonin Jihohin Arewa sun bada gudunmawar kayayyaki na miliyoyin Naira ga matan jami’an tsaro da ’yan kungiyar matsafan kabilar Eggon da akafi sani da Ombatse suka kashe a kauyen Alakyo da ke karamar Hukumar Lafiya a Jihar Nasarawa. An rarraba kayayyakin ne a wurin shakatawar manyan jami’an ’yan sanda da ke Lafiya a makon […]

Matan Gwamnonin Jihohin Arewa sun bada gudunmawar kayayyaki na miliyoyin Naira ga matan jami’an tsaro da ’yan kungiyar matsafan kabilar Eggon da akafi sani da Ombatse suka kashe a kauyen Alakyo da ke karamar Hukumar Lafiya a Jihar Nasarawa.
An rarraba kayayyakin ne a wurin shakatawar manyan jami’an ’yan sanda da ke Lafiya a makon jiya Kuma Uwargidan Gwamnan Jihar Nasarawa Hajiya Salamatu Umaru Al-Makura da takwararta ta Neja Hajiya Jummai Aliyu Babangida da ta Jihar Benuwai Misis Doshima Suswan ne suka mika gudunmawar a madadin matan Gwamnonin Arewar.
Da take jawabi wajen mika tallafin Hajiya Jummai Aliyu Babangida ta bayyana kisan jami’an tsaron a matsayin rashin imani, inda ta yi kira ga matan mamatan su dauki hakan a matsayin kaddara. “Mu matan gwamnonin Arewa muna jajanta wa Jihar Nasarawa game da aukuwar lamarin mai bakanta rai. Shi ya sa muka ga ya dace mu zo mu ba da tamu gudunmawa don taimaka wa kokarin mazajenmu don inganta rayuwar marasa galihu a kasa baki daya,” inji ta.
A nata jawabin Hajiya Salamatu Al-Makura ta bukaci al’ummar jihar su zauna lafiya da junansu don ba gwamnati damar ci gaba da inganta rayuwarsu. Ta nanata kudirin gwamnatin jihar na inganta rayuwar matan da aka kashe mazajensu hade da ’ya’yansu.
Hajiya Salamatu Al-Makura ta yi kira ga matan su tabbatar sun yi wa ’ya’yansu kyaukkyawar tarbiyya. “Mun zo ne domin mu jajanta muku kuma mu taimaka muku da wadannan kyaututtuka a wannan lokaci da kuke bakin ciki. Za mu yi namu ne kawai amma babban mai taimakawa shi ne Ubangiji Madaukaki,” inji ta.
Da take mayar da jawabi a madadin matan jami’an tsaron, Misis Rose Mika ta mika godiya ga matan gwamnonin Arewar dangane da karamcin inda ta ce za su yi amfani da su yadda ya dace. Ta yi kira ga gwamnati ta tabbatar an kamo an kuma hukunta makasan mazajensu.
Idan za a iya tuna a makon jiya ne kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa suka ziyarci Jihar Nasarawa inda suka ba matan jami’an tsaron Naira miliyan 100.