Matan Najeriya ba su iya soyayya ba – Saurayin bazawara Baturiya

Wani saurayi da wata bazawara Baturiya ta biyo shi daga kasar Amurka don ta aure shi, mai suna Isa Suaiman Isa ya ce matan Najeriya ba su iya soyayya ba.    Isa Sulaiman wadda Baturiyar da ta fito daga Jihar Kalifoniya a Amurka mai suna Jeanine Sanchez ta biyo shi har gidansu da ke Unguwar Panshekara […]

Matan Najeriya ba su iya soyayya ba – Saurayin bazawara Baturiya

Wani saurayi da wata bazawara Baturiya ta biyo shi daga kasar Amurka don ta aure shi, mai suna Isa Suaiman Isa ya ce matan Najeriya ba su iya soyayya ba.   

Isa Sulaiman wadda Baturiyar da ta fito daga Jihar Kalifoniya a Amurka mai suna Jeanine Sanchez ta biyo shi har gidansu da ke Unguwar Panshekara a birnin Kano da nufin kulla aure a tsakaninsu, Aminiya ta samu labarin cewa soyayya mai zafi ta kullu a tsakaninsu ne duk da bambancin kabila da addini da shekaru ta hanyar haduwarsu a shafin sada zumunta na Instagram.

A tattaunawarsa da Aminiya, saurayin ya ce ya karbi soyayyar Baturiyar bazawararsa Jeanine Sanchez hannu bibbiyu sakamakon dawowa daga rakiyar ’yan matan Hausawa da ya yi wadanda ya siffanta da cewa ba su iya soyayya ba.

A cewar saurayin wanda a baya yake gudanar da sana’ar askin baba “Mafi yawa ’yan matan Najeriya ko Arewa suna son mutum ne bisa wasu bukatunsu wadanda da zarar suka fuskanci mutum ba ya da abin da za su mora, to fa za su yi watsi da shi. Daga abin da ya faru da ni a baya, na yi soyayya da ’yan mata kusan hudu a lokuta daban-daban sai dai dukkan ’yan mata da na yi ban samu tsantsar soyayya daga wurinsu ba sai kan Jeanine.  Akwai wata ma daga cikinsu da take Jihar Zamfara. A wancan lokacin haka na tashi daga Kano na je Zamfara wajenta amma daga baya da ta fuskanci ba ni da abin da zan ba ta, sai ta rika yi min hanya-hanya har na gane abin da take nufi,” inji shi.

Mahaifin Isa, Malam Sulaiman Isa

Ya ce “A gaskiya na ji jiki a wancan lokaci, domin ba abu ne mai sauki ba kana soyayya da mace a lokaci guda ta juya maka baya.”

Game da bambancin da ke tsakanin soyayyar Hausawa da ta Turawa Isa Sulaiman mai shekara 23 ya ce matan Turawa idan suka ce suna son mutum to da gaske suke yi. “Idan Baturiya ta nuna tana sonka to da gaske suke lamuransu ba karya ko yaudara a ciki. Amma yawancin yaranmu a nan ba sa son mutum sai sun ga yana da kudi wanda za su mora. Har matan ban da a nan Najeriya wa za a samu ya hada soyayyar mutane da dama a lokaci guda. Ba abu ne mai wuya ka samu budurwa tana da samari uku zuwa hudu ba. Amma su Turawa ba za su iya yin hakan ba,” inji shi.

Ya musanta rade-radin da ake yi cewa wai tsohuwar budurwarsa ta nuna rashin amincewarta game da soyayyarsa da Baturiyar inda ya ce tsohuwar budurwar tasa har kiransa ta yi a waya tana taya shi murna. “Eh ina da budurwa mai suna Nafisa a Unguwar Hotoro mun dade da rabuwa tun kafin haduwarmu da Jeanine, zan iya cewa na kusa shekara biyu ba ni da budurwa. Lokacin da ta samu wannan labari sai ta kira ni a waya ta yi min murna tare da fatar alheri. Har ma ta roki cewa tana son su hadu da Jeanine. Sai dai abin bai yiwu ba saboda fama da zazzabi da ta yi, inda muka hakura sai zuwa wani lokaci na daban.”

Isa ya ce akalla sun shafe shekara daya suna soyayya da bazwawarar Baturiyar tasa inda ya ce sai a wannan lokaci ne ta zo, “Kamar yadda na bayyana cewa mun hadu ne a dandalin sada zumunta na Instagram inda na taimake ta daga wadansu mutane da suka so cutarta wasu makudan kudi. To ganin yadda na taimaka mata ne ta yaba da hankalina da gaskiyata har muka fara gaisawa da juna daga bisani muka kulla soyayya mai karfi,” inji shi.

Game da iya nuna soyayya ya ce “Ai ba za ki hada ba, domin ita Baturiya idan ta fara son mutum to fa da gaske take yi za ta yi duk kokarinta wajen ganin sun rayu tare. Kuma sun iya nuna wa mutum soyayya ba kamar matanmu na nan ba. Ki duba yadda wannan mata ta taso tun daga uwa duniya domin kawai mu hadu. Haka ta kashe makudan kudi a wanann tafiyar kin san ba karya take ba.”

A tattaunawarsa da Aminiya mahaifin saurayin wanda tsohon dan sanda ne, Malam Sulaiman Isa ya ce a matsayinsu na iyayen saurayin ba su da abin cewa sai dai su sanya wa lamarin albarka, lura da cewa komai na rayuwar mutum Allah ne ke tsarawa. “Lokacin da Isa ya yi mana bayani game da wannan mata (Jamila sunan da na sanya mata ke nan), ba mu nuna kyama ga lamarin ba. Saboda addinin Musulunci ya yarda namji ya auri wacce ba Musulma ba. Haka dan zamanmu da ita na wadanann kwanaki mun yaba da halayenta, domin zan iya cewa ita mutum ce mai son jama’a da girmama su, ba ta kyamar mutane. Don haka muna yi musu fatar alheri.”

Sai dai Malam Sulamian ya ce duk da cewa ya amince da batun auren dansa da Baturiyar amma ya gindaya wasu sharudda da sai an cika su sannan auren zai yiwu, “Kin san shi aure dole ne sai mutum ya yi bincike don haka yanzu mun nemi Ofishin Jakadancin Amurka ya bincika mana wace ce ita. Mun nemi hakan ne da hadin gwiwar Hukumar Tsaron Kasa ta DSS.  Har ila yau mun sanya cewa dole ne a bar shi ya yi addininsa na Musulunci ba tare da kuntatawa ba. Kuma za a bar shi ya nemi ilimi. Ba mu yarda a sanya shi cikin wasu kungiyoyi ba. Har ila yau muna so ya zama yana girmama kasarsa. Idan muka samu bayanai masu kyau a kanta babu komai mun amince a yi auren.”

Da aka tambaye shi yadda a matsayinsu na iyaye suka amince su bar dansu ya tafi wata uwa duniya ba dangin iya ba na baba, sai Malam Sulaiman ya ce “Ai wannan kamar yadda kowane uba yake barin dansa ya tafi karatu kasar waje ne. Duk da cewa akwai dan bambanci kadan. Duk da cewa ina da ’ya’ya da yawa, wannan ba shi yake nufin ban damu da dana ba. Muna son danmu kuma za mu rika bibiyar halin da yake ciki. Kuma ko ya tafi a matsayinmu na iyaye za mu rika dora shi kan tafarki yadda zai kiyaye addininsa da mutuncin kasarsa. Kuma  ba na shakkar cewa matar za ta iya raba mu da shi. Shi yaro ne mai son iyayensa da ’yan uwansa. Ina da tabbacin duk inda ya je sai ya neme mu.”

Mahaifin ya ce tsira shekara har 23 tsakanin masoyan ba abu ne da zai hana yiwuwar auren ba. “Duk da cewa ta girme shi domin ita tana da shekara 46 shi kuma yana da shekara 23, wannan ba zai hana auren ba, domin ma hakan koyi ne ga Annabinmu Muhammadu (SAW) don haka kin ga ma ya yi koyi da Sunnah.”

Game da gayyatarsu da Hukumar Hisba ta yi Malam Sulaiman ya ce “Hukumar Hisbah ta gayyace mu ta ba mu shawara game da makomar addinin danmu don kada bayan ya tafi ya rasa addininsa. Sun nuna masa muhimmancin riko da addini da sauransu. Kuma ita ma Hukumar Hana Safarar Mutane ta kira mu inda ta gargade mu kan muhimmancin yin bincike a kan lamarin kafin mu amince gudun kada a karshe abin ya zama wata hanyar fataucin mutane.”

Duk kokarin Aminiya na  tattaunwa da Jeanine Sanchez wacce ke da ’ya’ya biyu ya ci tura domin ta ki cewa komai inda ta ce abin da ta sani shi ne tana son Isa kuma za ta aure shi.

Abin jira a gani dai cikar wadancan sharudda na iyayen saurayi Isa da kuma zuwan watan Maris da aka sanya za a yi aure a Kano.