Matan Najeriya za su dara idan mijina ya zama Shugaban Kasa – Matar Atiku

Ta ce maigidanta zai mayar da hankali a kan bangarori uku na inganta rayuwar matan Najeriya

Matan Najeriya za su dara idan mijina ya zama Shugaban Kasa – Matar Atiku

Uwargidan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Hajiya Rukayya Atiku Abubakar ta ce mijinta ya yi wa matan Najeriya tanade-tanaden da ba za su yi da-na-sani ba idan suka zabe shi a zaben 2023 mai zuwa.

A cewarta, maigidan nata ya yi wa mata gagarumin tanadin inganta kowane bangare na rayuwarsu, musamman ta fannin ilimi da lafiya da kuma samar musu da sana’o’i.

Ta bayyana hakan ne a Kano yayin wani gangamin wayar da kan mata kan batutuwan da suka shafi siyasa a jihohi guda bakwai na shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya.

Matar tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ta kuma ce, “Kowa ya san maigidana ya shahara da inganta rayuwar mata, ko da siyasa, ko ma ba lokacin siyasa ba. Kowa ya san shi yana taimakawa.

“A jihar Adamawa alal misali, ya bude makaranta tun daga matakin Nazire har zuwa jami’a, kuma ya dauki yara biyar-biyar daga kowace Karamar Hukumar jihar dauki nauyin karatunsu a jami’a,” inji ta.

Ta kuma ce idan suka kafa gwamnati, ba za su yi watsi da mata ba sabanin yadda ta ce wasu ’yan siyasar na yi.

“Ina sake jan hankalin mata, saboda sau da yawa ana cewa su fita su yi zabe, amma idan an ci zaben sai a manta da su. Amma mu ya kamata su ga irin ayyukan da maigidana yake yi a kullum don su fahimci cewa ya banbanta da sauran,” inji ta.

Ta kuma yi alkawarin inganta asibitoci da harkar lafiya, matukar suka lashe zabe mai zuwa, don magance kalubalen da matan ke fuskanta wajen kula da lafiyar iyalansu.

Hajiya Rukayya ta kuma ce tuni ta samar da cibiyoyin koyar da sana’o’i don tallafa wa mata da bunkasa rayuwarsu da kuma tabbatar da ci gabansu.

Da take nata jawabin, Shugabar cibiyar wayar da kan mata akan muhimmancin zabe da zabar shugaba nagari ta Grama Media Action Arewa, Malama Hadiza Balanti, ta ce, a bangarensu, sun daina yarda mata su fito cikin tsakar rana da yunwa da kishirwa su yi zabe, amma da zarar an ci zabe sai a manta da su.

Ta kuma kara da cewa “Mun bi lungu da sako na unguwannin da ke kwaryar Kano da suka hadar da unguwanni 143, da wasu bangarori na Kananan Hukumomin da ke wajen birni, kan cewar a wannan karon mata kada su yarda da kudi ko dadin baki na wasu ‘yan siyasar ko kuma rubuce-rubuce a takardu ya rude su, sannan su zabi wanda ya san darajarsu.”