Matan Saudiyya na zuwa asibiti don neman haihuwar maza

Mata da dama a kasar Saudiyya na bukatar haihuwar ’ya’ya maza, wai a tunaninsu ta haka ne zuria’arsu za ta ci gaba da yaduwa, tare da jagororin iyalai, kamar yadda jaridar Arab News ta ruwaito. Wadannan mata da ke fafutikar ganin sun haifi da namiji, sun hada da wadanda suka haifi ’ya’ya mata, duk da […]

Matan Saudiyya na zuwa asibiti don neman haihuwar maza
Matan Saudiyya na zuwa asibiti don neman haihuwar maza

Mata da dama a kasar Saudiyya na bukatar haihuwar ’ya’ya maza, wai a tunaninsu ta haka ne zuria’arsu za ta ci gaba da yaduwa, tare da jagororin iyalai, kamar yadda jaridar Arab News ta ruwaito.

Wadannan mata da ke fafutikar ganin sun haifi da namiji, sun hada da wadanda suka haifi ’ya’ya mata, duk da haka suke da tururuwa zuwa asibitoci don neman taimakon likitoci kan yadda za su haifi namiji.
Fawzia Al-Shamakh, wata kwararra kian abin ya shafi tunanin da dabi’un dan adam, da ke Kwalejin Dar Al-Hekma, ta byyana cewa matan ana nuna irin wannan dabi’ar ne saboda a kasar nan an dauka cewa, su ke da kyakkyawar makoma da samun matsayin jagorancin iyalansu.
“Shi yasa macen da aka gano tana dauke da juna biyu na da namiji, sai ta cika da kuzari da annashuwa, tare da gamsuwar cewa ta samu matsayi na daraja,” inji ta.
Shamakh ta ce akwai bukatar matan Saudiyya su yi kokari wajen sauya irin wannnan tunanin, ta hanyar tabbatar da cewa su ma za su iya rika mukamai a kowace irin masana’anta.
Shi kuwa Fahd Salman, wani kwararren likita a fannin kula da lafiyar mata masu juna biyu da barbarar kwayayen haihuwa ga bakarariya, ta yadda za samu juna biyu, ta haihu, ya ce jinsi jariri ya danganta ne ga kwayoyin hlittar iyayensa. Babu wata dabara da ke da tabbaci samun nasarar biyan bukatun matan.
Sai dai, a cewarsa, a da anja amfani da dashen kwayoyin halittar jinsi, ita ma waccan dabarar ba a cika smaun nasara ba. Kuma har yanzu akwai asibitoci da dama a masarautar da ke amfani da irin waccan dabarar.
Mazen Bishara, shi ma wani kwararren likitan kula da lafiyar masu juna biyu da ke birnin Jeddah, ya ce ana yawan bijiro da wadannan bukatu (na neman haihuwar da namiji) a kasar Saudiya. Fiye da sauran kasashen duniya. Domin mutane da daman a ganin cewa kwararrun likitoci za su iya jirkita jinsi jariri, a cewarsa.

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume