Matan Saudiyya sun shigar da kararraki 823 kan hana su auren wadanda suke so
’Yan matan Saudiyya sun kai karar magabatansu a hukumomin Haia da kotuna, wadanda aka kimanta yawansu har 823, bisa tuhumar iyaye da masu riko da ke hana mata auren wadanda suka kwanta musu a rai. Kamfanin Dillancin Labarai da sauran kafofin yada labarai sun ruwaito labarin, wata Likitar fita, wadda ke da shekara 42, wadda […]
’Yan matan Saudiyya sun kai karar magabatansu a hukumomin Haia da kotuna, wadanda aka kimanta yawansu har 823, bisa tuhumar iyaye da masu riko da ke hana mata auren wadanda suka kwanta musu a rai. Kamfanin Dillancin Labarai da sauran kafofin yada labarai sun ruwaito labarin, wata Likitar fita, wadda ke da shekara 42, wadda ta kai karar mahaifinta, saboda ya ki amincewa da mai neman aurenta, kuma albashinta na shiga ne cikin asusun ajiyarsa a banki.
Wannan Likitar da ke aiki a birnin Madina ta fahimci cewa mahaifinta da mai rikonta duk sun saba wa shari’ar Musulunci, inda suka tursasa mata zaman gwagwarci. Wai duk suna aikata hukuncin ne a karkashin wani tsari da suke kira “adl.” Don haka ta gabatar shi a kotu, karar da ake ta mahawara a kanta.
Wata marubuciya da aka sanya wa takunkumin rubutu a jaridu da maujallu ko furta ra’ayinta ta wata kafar yada labarai, al-Hawaidar, mai fafutikar hakkin mata, ta bayyana wannan doka, a matsayin “dokar da ta dauki mata tamkar wasu ananan yaran dab a su balaga ba.” Ta kuma ce mace ko wayar salula za ta saya, ba za ta yiwu ba, ahr sai ta samu izinin magabacinta namiji.
Ba da dadewa ba aka Jaridar Al-Hayat da kungiyar Fafutikar ‘’Yancin dan Adam, sun samu kararraki 30 na wannan doka ta adl, a wanan shekarar. Kuma an kafa shafin facebook da aka yi wa lakabi da “enough adhl,” a karkashin kulawar Farfesan Jami’a da wadanda suka cutu, wadanda yawansu ya kusa kaiwa dubu 800. Wannan kungiya ’ya’yanta sun kai mutum 421, wadanda ke fafutikar ganin an hukunta mazan da suka hana ’yan mata auren mazan da suke so.
An dai kiyasta akalla mata fiye da miliyan hudu, wadanda shekarunsu ya wuce 20 da har yanzu ke zaman gwagwarci, a kasar da ke da yawan mutum miliyan 24 da dubu 600. karin ban takaicin ma, wasu alkalan matan da suka kai kara suke hukuntawa.