Matan shugabanni iyayen al’umma ne –Dokta Zainab Abubakar Atiku
Dokta Zainab Abubakar Atiku ita ce matar Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu. Babbar likitar yara ce, ta kware kan kula da lafiyar yara. Tana da asibitin yin gwaje-gwajen jikin dan adam kuma tana da shirye-shirye na musamman game da inganta rayuwar mata da kananan yara a Jihar Kebbi. Ta nemi a […]
Dokta Zainab Abubakar Atiku ita ce matar Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu. Babbar likitar yara ce, ta kware kan kula da lafiyar yara. Tana da asibitin yin gwaje-gwajen jikin dan adam kuma tana da shirye-shirye na musamman game da inganta rayuwar mata da kananan yara a Jihar Kebbi. Ta nemi a yi karatu don a fita daga jahilcin da ya dabaibaye Arewa.
Tarihin rayuwa:
Sunana Zainab Abubakar Atiku Bagudu. Ni mutuniyar Zamfara ce, maigidana mutumin Jihar Kebbi ne, kuma shi ne Gwamnan Jihar Kebbi a halin yanzu. An haife ni a Legas. Na yi karatun firamare da na sakandare a Legas. Na yi sakandaren kueens College. Da na gama sai na dawo Sakkwato. Duk da yake ba ni da niyyar gigaba da karatu amma Kawuna ya ce dole sai na yi karatun likitanci. Na yi zaman koyon aiki a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya.
Bayan na kamala sai na wuce kasar waje na cigaba da karatuna, inda na kware akan kula da lafiyar yara amma na shiga bangaren bincike da gwaje gwaje. Abinda nake nufi shi ne aikin da muke yi ya fi shafar bangaren cutar dake damun mutum.
Na dawo gida Nijeriya sannan na fara aiki a asibitin Garki da ke Abuja. Mu muka fara aiki a lokacin da asibitin ya koma na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da wasu likitoci masu zaman kansu. Yanzu haka ina da asibiti aAbuja inda nake aiki.
A matsayinki na matar gwamna kuma likita, ya za ki mayar da hankali kan kula da mata da kuma kananan yara a Jihar Kebbi?
A gaskiya in kana matar wani babban shugaba dole ne ka zama tamkar uwa ga al’umma musamman ga mata da kananan yara. Kuma ka ce ba za ka yi komai ba, za ka ga mata da suke bukatar taimako sun tunkaro ka. Mu a Jihar Kebbi muna da matsalar yara mata da dama da ba su zuwa makaranta, saboda zan fi mayar da hankali ta wannan bangaren.
Ni ba wai zan fito da wani shiri sabo ba ne amma zan yi aiki da kungiyoyi da dama don mu hada hannu wajen karfafa masu gwiwa a kowace karamar hukuma 21 da muke da su a Jihar Kebbi da taimakom maigidana mai girma Gwamnan Kebbi. Alal misali kamar a Birnin Kebbi ana karfafa masu wajen neman ilimi in sun gama sun tashi aure sai a ba su aiki ko a koya masu sana’a , to wannan ne zan yi a duk kananan hukumomin Jihar Kebbi.
Sannan akwai shiri akan marayu. Dalilin ciwon kanjamau da kuma ’yan gudun hijira wanda yake a nan Jihar Kebbi muna da su da dama inda haka ya haifar da yara marayu da yawa. Gwamnatin Jihar Kebbi tana taimakonsu ta wata hukuma da ake cewa Arabic Board inda take daukar nauyin karatunsu sannan akwai wata kungiya da take aikin taimaka wa wadannan marayu inda suke neman masu son taimakawa su yi aiki da su. Ni ma sun sanya ni a ciki, ita ma uwargidan shugaban kasa Hajiya A’isha Buhari tana da sha’awa akan wannan aiki na taimakawa marayu a J ihar Kebbi.
Sannan mata da yawa a kasar nan suna rasa rayukansu ne a wajen haihuwa, to akwai abinda muke yi na raba kayayyakin haihuwa don a rika tallafa musu musamman ga wadanda ba su da karfi. Don wasu matan ba sa zuwa asibiti haihuwa ne saboda rashin kayayyakin haihuwa. Wasu kuma al’adarsu ce take hana su zuwa asibiti haihuwa.
Mukan shiga ko’ina don fadakarwa kan rigakafi da muhinmancin bai wa jariri nonon uwa zalla wanda ya an kare jaririn daga daukar cututtuka iri-iri.
Mene ne burinki?
Burina shi ne na ga kasata Najeriya musamman ma bangaren Arewa ta samu cigaba a bangaren ilimi. Saboda idan ba mu natsu muka nemi ilimi ba, muka kawar da jahilci ba, abubuwanmu da yawa ba za su taba tafiya daidai ba. Musamman ma mata idan ba su tsaya suka nemi ilimi ba, ko su yi yaki da jahilci ba to akwai matsala. Ba na cikin masu cewa wai gwamnati yakamata ta yi kaza kafin mutane su himmatu. Amma su kansu mutane ba sa yi wa kansu adalci. Za ka tarar da malami ba ya zuwa aji akan lokaci, wasu ma ba kullum suke zuwa makaranta ba, haka abin yake ga ma’aikatan gwamnati, wasu ba sa zuwa a kan lokaci, wasu ba sa zuwa kwata-kwata sai wata ya yi nisa da dai sauransu To ka gaya mini ta yaya abubuwa za su tafi daidai a kasar nan. Muna fata Allah Ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali don mu samu bunkasar rayuwa a kasar nan.
Halayen mata dake burge ki:
A gaskiya ina son in ga mace mai ilimi wacce ta san abinda take yi, kuma tana amfani da shi. Ban son ganin mace ta zama kamar ballagaza, wacce ba ta san ciwon kanta ba.
Mene ne sirrin zaman aure?
A gaskiya mace ita take rike aure. Abinda zan ce shine mata su fahimci halayen mazajensu. Idan kika gane halin mijinki, to kin gama komai kin san yadda zaki zauna da
Matan shugabanni iyayen al’umma ne –Dokta Zainab Abubakar Atiku
shi lafiya. Za ku ji ana cewa ma’aurata su yi hakuri, to an fi jaddada wannan kalma a wajen mace, don ita ce mai rike da gida. Don hata shi kansa mijin da ’ya’yan suna karkashin kulawar mace ce. Don haka yana da kyau mace ta karanci halin mijinta don ta san yadda za ta zauna da shi lafiya. Kuma yakamata mace ta rika tsaftace gidanta da kanta da ’ya’yanta da kula da tarbiyyarsu. Sannan ta rika yin addu’a Allah Ya taimaka mata a duk abubuwan da take yi. Hakan shi zai sa ka ga komai ya rika tafiya daidai.
Ta yaya kike hada aikin asibiti da kuma zama matar gwamna?
To Allah Ubangiji Ya yi wa mata baiwa mai yawan gaske. Ko mace ba ta aiki in ka je gidanta za ka ga yadda take yin ayyuka da yawa a lokaci guda. Za ka ga ta shiga kicin tana girki sannan ita ce wanki da wanke-wanke, in yaro ya tashi ta bashi nono,ta hada masa abincinsa daban kuma a lokaci guda tana girka na gida. Sannan ita ce kai yaro asibiti da sauransu, duk wadannan abubuwa za ka ga tana yi ba tare da ta gaza ba.
Hada ayyuka biyu ko fiye a lokaci guda a wajenmu ba wani sabon abu ba ne. Idan na tafi Abuja wajen aiki, maigidana yana wajen aiki, bayan kwana biyu in na dawo Birnin – Kebbi akwai abubuwa da dama da nake cigaba da yi. Mutane kan ziyarce ni, ni ma kuma ina kai musu ziyara don sada zumunci. Wadansu suna bukatar taimako, don haka dole a tallafa musu, don haka nake kokarin ganin na tallafa wa marasa karfi don na inganta rayuwarsu.
Wace hanya kike bi don samun shakatawa?
Mukan yi tafiya mai dan nisa ko yin atisaye tare da yin wasa da yara a gidana. Ina sha’awar yin shuke-shuke don haka nake zagawa ina yin shuka da kaina, ba tare da na sanya kokwa. Kuma a mafi yawan lokuta ni ke ba shukokin da na yi ruka da kaina don cigaga da raino. A wasu lokuta in ka ga ina fada da masu aikina, to sun yi sakaci da kula da shukokin da na yi ne, don ina son shuka sosai a rayuwata.
Ina kika fi sha’awar zuwa don yin hutu?
Da na kance ina sha’awar zuwa wurare da dama, amma babu inda na fi sha’awar zuwa da ya wuce Makka. Da zan samu dama da na koma can da zama kwata-kwata. Abinda ya sa nafi kaunar zuwa zuwa makka shi ne na kan ji wani irin kwanciyar hankali da natsuwa musamman in na kasance a kusa da Ka’aba. Ba zan ce na fi kowa addini ba , ko kuma ni wata ustaziyace. Kawai na fi natsuwa da kwanciyar hankali ne idan ina kasar Saudiya.