Matan shugabannin kasa: Salonsu da tasirinsu

Remi Tinubu ta kauce wa duk wani abu na siyasa da ba dole ba a matsayin Uwargidan Shugaban Kasa.

Matan shugabannin kasa: Salonsu da tasirinsu

Nijeriya ta cika da fitattun matan shugabanni, inda suka rabu da salon da mata suka saba na matan shugabannin siyasa.

A cikin shekara 25, kasar nan ta samar da shugabanni wadanda matansu suka nuna juriya, hangen nesa, sadaukarwa da kuma manufar yin tasiri ga ’yan uwansu mata da kuma sa’a, ga ’ya’ya mata.

Uku daga cikin matan shugabannin kasa biyar na Jamhuriya ta huɗu sun taka rawa a bayan fage a matsayin masu juya akalar gwamnati, inda suka bullo da ayyukan tallafawa a matsayin matan gwamnoni kafin su dauki matsayi mafi girma a matsayin matan shugabannin kasa.

Sauran biyun da ba sa cikin wannan rukuni su ma fa sun haskaka.

Dukkan ayyukan sun tsara ne don wasu rukunai na al’umma – mata, yara da masu rauni cikin al’umma.

Maimakon gina harsashin da magabata suka kafa, kowace mace ta kafa wani aiki na musamman da ya bambanta zamansu a Aso Rock, wanda zai yi wuya a goge shi ko da sun sauka daga mulki.

Ɗaya daga cikin abin da ke kawo shigar wadannan mata masu karfi a harkokin siyasa na iya yin tasiri mai dorewa kan rawar da mata ke takawa a siyasa.

Daga cikin matan da suka yi tasiri a harkokin siyasa a Aso Rock ta rasu a fadar mulkin.

Stella Obasanjo

Kafin a yi masa afuwa kuma a ba shi tukuicin shugabancin kasa, ba a san Stella Obasanjo ba ko kadan.

An haifi Stella Abebe a ranar 14 ga Nuwamba, 1945 a zuriyar Shugaban Kamfanin UAC dan kasa na farko.

Misis Stella Abebe ta yi digiri na farko a fannin Ingilishi a tsohuwar Jami’ar Ife, yanzu Jami’ar Obafemi Awolowo.

Ta koma Ingila inda ta yi karatu a fannin Inshora, amma daga baya ta zama sakatariya a ofishi.

Wasu masana tarihin rayuwa sun danganta matakin da Obasanjo ya dauka na nada Stella a matsayin uwargidansa ga biyayyarta da goyon bayan da ta bai wa mijinta a lokacin da yake fama da rashin lafiya da kuma tsare shi a gidan yari. Dagewarta ya biya.

Stella ta shiga cikin harkokinmu na siyasa da karamin tsarinta, tsayuwar dakanta da karfin kudurinta sun jawo sunanta ya daukaka a tsakaninmu da tarihin siyasa.

Da kafa shirinta na Gidauniyar Kula da Yara (Child Care Trust), ta mayar da hankali kan yaki da bautar da yara da kula da yara nakasassu da yaki da cin zarafin mata da kaciyar mata, wadda ta kafa cibiyar a Bwari, a wajen Abuja.

Sai dai ba ta rayu don ganin tasirin aikinta ba. Abin takaici, goyon bayanta ga al’amuran da suka shafi yara ne zai haifar da rikici na farko kuma kuma na karshe da kafofin watsa labarai.

A watan Mayun 2005, an kama mawallafin wata jarida da ke Legas bisa umarnin Shugaban Kasa.

Laifinsa shi ne ya bayar da wani labari da aka ce an kebe wa wasu ’yan uwan marigayiyar Uwargidan Shugaban Kasar, wasu gidaje da gwamnati za ta yi gwanjonsu.

Kurar da waccan rahoton ya haifar ta lullube aikin kula da yara na Uwargidan Shugaban Kasar.

Daga baya an samu labarin cewa an kai ta wani asibiti mai zaman kansa mai suna Marbella da ke garin Puerto Banus na kasar Spain, inda daga baya jaridun Spain suka bayyana da tiyatar rage tumbi ne aka yi mata.

Ba ta rayu ba bayan yi mata wannan aiki, kuma ta zama mace ta farko kuma matar Shugaban Kasa ta farko da ta rasu a Fadar Shugaban Kasa.

Ga mutane da yawa, za a iya tunawa da Stella ce kan alherinta, natsuwa da iya shigar kaya.

Wani mai shafin sadarwar zamani mai suna #oguupdate ya taba bayyana salon sanya tufafinta da ‘peplum’ wanda ke nufin tana rufe muhimman sassan jikinta ta bar sauran jikin.

Salon gashin afro na Stella ta bar shi ba rufi ko ta rufe kadan, koyaushe na tunatar da rayuwar soja na mijinta na sa kayan gargajiya.

Ya’alla an yi ado da yadin leshi ko adire, Stella na tsantsara ado salo iri-iri da shigar al’ada da suke tasiri ga matan zamaninta.

Rasuwarta ba zato ba tsammani ta rufe wannan juyin juyahali a salon sanya tufafi.

Turai ’Yar’aduwa

Magajiyar Stella ‘Turai Yar’adua’ ta bambanta da ita.

Yayin da ta kasance a bayyane a fagen siyasa, Turai ta kasance a baya, haka a salon shiga da bayyana a gaban jama’a, kamar yadda addini da al’adun mijinta suka koyar.

Hajiya Turai ta samu digirinta a fannin Ingilishi a Jami’ar Ahmadu Bello, inda ta kafa tarihin zama matar Shugaban Kasa da ke da ilimi.

Kamar marigayi mijinta, Turai an santa da sha’awar ilimi, ta fara aiki ne da koyarwa.

Kuma ta sadaukar da kai wajen kula da marasa galihu, daga baya ta zama zakaran gwajin dafi wajen ganin mutane na yin gwajin cutar kansa da kansu a Nijeriya.

Ta kafa Cibiyar Yaki da Cutar Kansa ta Duniya a kan wani fili mai cike da ce-ceku-ce a Titin T-junction a hanyar Abuja zuwa Gwagwalada.

Burinta shi ne “A tashi tsaye” don yakar ciwon kansa da illolinsa ga kasa, kamar yadda ta fada lokacin kaddamar da wannan aiki.

Duk da cewa ba a iya gane tasirinta a gwamnatin mijinta, an yi ta rade-radin cewa tana da ta cewa wajen zaben wasu a ministocin mijinta.

A kan kwalliya, Adaora Nwangwu ta bayyana salon Turai a matsayin ‘mai sauki,’ tare da bayyana cewa ya kunshi “Zani, lullubi da gyale” wanda aka yi shi da ‘fure’ da take yafawa a kafadarta.

Takaitaccen zamanta a matsayin Uwargidan Shugaban Kasa tare da sanin halin mijinta na iya hana Nijeriya wata dama ta fito da wani sananne salon.

Ba a ji wani labari sosai a kan aikinta na yaki da cutar kansa ba bayan rasuwar mijinta da ya tilasta mata komawa cikin iyalinta a Katsina.

Dame Patience Jonathan

Uwargidan Shugaban Kasa na uku bayan mulkin soja, Dame Patience Jonathan ta fi shahara da jagwalgwalon magana da kuma yawan kutsa kai a cikin al’amuran kasa fiye da yadda aka san ta a matsayin fitacciyar mai kwalliya.

Da yawa mutane na bayyana Patience da sarauniyar karaga da ke kullawa da kwacewa a bayan fage.

Wani abu da masana tarihinta suka nuna shi ne ita ce ta fi ‘sanuwa’ a matsayin Uwargidan Shugaban Kasa, inda ta samu digiri na daya da na biyu da na uku a Jami’ar Fatakwal.

Masu adawa da ita za su rantse cewa wadannan digirori na Ingilishi ba su yi wani alfanu ba, in aka lura da yadda take gaggatsa harshen.

An san ta da karan-tsaye ga tsarin jumloli da gininnsu da salo da ilimin harshe.

Kamar mijinta, tana iya zama Uwargidan Shugaban Kasa da aka fi suka, inda mafi yawan sukar ta fi karkata a kan kassara harshen Ingilishi da take yi.

Dokta (Misis) Jonathan ba ita kadai ce Uwargidan Shugaban Kasa da aka mayar da ita a baya ba.

Ta kasance daya daga cikin jiga-jigan ’yan siyasa a jiharta da Abuja a tsawon shekara shida da suka yi a babban birnin kasar.

Aikin tallafinta, Women for Change and Initiatibe da a takaice ake kira W4CDI, ya mayar da hankali ne kan ceto macen Nijeriya, yaki da cin zarafi da tozarta mata da kuma daukaka matsayin ’ya-mace.

Sai dai wannan shiri nata ya ci karo da matsayinta lokacin da aka sace ’yan matan Chibok, inda ta fito fili ta nuna shakku kan gaskiyar faruwar lamarin da sahihancinsa.

Sauran manyan muradun shirin sun hada da tabbatar da bin ka’idojin da Majalisar Dinkin Duniya na kasancewar mata su kai kashi 25 cikin 100 a harkokin mulki da tsara manufofi.

Ta samu lambobin yabo a gida da waje da yawa da kuma karramawa saboda ayyukanta, sai mukaman sarauta da yawa.

Ba a lura da salon sa kayan da ta kirkira ba duk da cewa tana shiga mai kyau, tsafta da kuma mutunci.

A’isha Muhammadu Buhari

Daga fitattun dangi zuwa gabanin mukamin Shugaban Kasa, A’isha Buhari ta fito ne daga tsarin bin al’ada da kuma abin da aka koyar da ita a makarantar gida zuwa takardun satifiket na kasshen waje a wajen gyaran jiki da kwalliya daga fitattun cibiyoyin ilimi a Ingila da Faransa.

Ta kara da digiri a fannin harkokin mulki daga Jami’ar Ambrose Alli da ke Jihar Edo.

Marubuciya a fannin da ta yi karatu, Hajiya A’isha Buhari ta ki komawa sahun baya a harkokin siyasa da mijinta ya so ta yi a matsayin matar aure kuma ta tilasta masa barin ofishin Uwargidan Shugaban Kasa da ake kyautata zaton wasu masu zaman kansu ne suka ɗauki nauyi.

Tasirinsa a siyasa ya fito fili, inda ta rika tsoma baki a harkokin siyasa da salon mulkin mijinta.

Ta zama mai suka da goyon baya, tana takalar kutse a tsakanin ’yan gaban goshin mijinta da kuma jam’iyya a matakin kasa.

Fafatawarta da surkanta ta sa ta kara kaimi a fagen siyasa yayin da take sukar ministoci da hukumomin gwamnati da ba su da aiki.

Shirin A’isha Buhari mai suna, Future Assured, an yi shi ne don magance batutuwan da magabatanta suka zayyana a cikin shiryeshiryensu – don jin dadin yara, mata da masu raunin cikin a’umma.

Kasancewarta mai magana, ta sha suka bayan da aka gano cewa ta bayar da umarnin kamawa tare da tsare wani mai amfani da kafafen sada zumunta wanda ya ce uwargidan Shugaban Kasar ta zama ‘Runtumemiya’ bayan da ta ci kudin kasa.

Surutan da jama’a suka rika yi sun tilasta mata ta ‘yafe’ wa mai laifin tare da ba da umarnin sake shi.

Uwargidan Buhari ta shafe karshen zamanta a wajen Nijeriya.

Sanata Oluremi Tinubu

Misis Tinubu ta zama Uwargidan Shugaban Kasa ta uku a sabon zubin dimokuradiyya wacce ta dandani Uwargidan Gwamna a matakin jiha.

Mijinta, kamar na Patience da Turai, sun kasance gwamnonin jihohinsu kafin su kai ga babbar kujerar.

Baya ga zama a inuwar siyasar mijinta, Misis Tinubu ’yar siyasa ce a kanta, inda ta wakilci Legas ta Tsakiya a Majalisar Dattawa a karkashin Jam’iyyar APC, sau uku a jere.

Wannan wani abu ne da ya tabbatar da goyon bayan da mijinta ya ba ta a daidai lokacin da take son yin ritaya ta fuskanci tarbiyyar ’ya’yanta.

Mahaifiyar mai shekara 63 ta samu digiri na farko a fannin kimiyyar koyarwa a Jami’ar Ife da takardar shaidar ilimi ta kasa (NCE) a fannin tsirrai da dabbobi daga Kwalejin Ilimi ta Adeyemi.

A matsayin Uwargidan Gwamnan Jihar Legas, Misis Tinubu ta kafa Gidauniyar New Era.

An bangaren addini, an daga matsayin Remi zuwa fasto ta farko a Cocin Redeemed Christian Church of God, (RCCG); cocin da aka sani da babban tasiri a fagen siyasa da ya ba ta zama Uwargidan Shugaban Kasa.

Misis Tinubu na fadin ra’ayinta ne ba tare da tantama ba, lamarin da a wasu lokuta kan sanya ta cikin matsala a fagen siyasa kamar a lokacin da ta ce ba za a amince da Ibo ba, saboda ba su kiyaye maganarsu ta biyayya ga jam’iyyar da ba wani daga cikinsu ya jagoranta ba.

Oluremi Tinubu ’yar kabilar Itshekiri da ta tashi a Legas. Sabon shirinta na da sunan The Renewed Hope Initiatibe (RHI).

Ta kirkiro shi ne don kula da bukatun mata, matasa da yara.

Ta bayyana noma, ilimi, karfafa tattalin arziki da tallafa wa jama’a a matsayin muhimman fannoni da za ta mayar da hankali.

Ta ce tallafin da za ta yi zai fito ne daga “kudin da ba a kashe ba daga asusun yakin neman zaben 2023” bayan haka tana fatar samun kudade daga “kungiyoyi masu ba da taimako na kasada-kasa da kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida.”

Ta samu goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. Misis Tinubu ta iya cancada ado, kuma ta fi son salon sutura mai sauki wadda a lokaci guda ke jan hankali.

Tana baje kolin aso-oke ko ofi da aka saka a cikin rigunanta, amma wani lokacin tana yafa mayafi a kan kayanta idan bukata ta taso.

Shekara guda kacal a kujerar shugabancin mijinta, a jingine batun tasiri da shirinta zai yi ga harkokin siyasa zuwa lokacin da zai kammala wa’adinsa na farko.

A yanzu, Misis Tinubu ta kauce wa duk wani abu na siyasa da rigima da ba dole ba a matsayin Uwargidan Shugaban Kasa.

A 2023, ta yi bikin yaye rukunin farko na waɗanda suka amfana daga shirinta na RHI.