Matan Sin na kwanciya a falalen dutsen don maganin cututtuka

Kafar sadarwa ta Hket.com ta ruwaito labarin yadda mata a yankin shaandi na kasar Sin ke kwanciya a falalen dutse don maganin cututttuka. Gungun matan wannan yanki kanj samu falalen dutsen da ya sha kunar rana. Ko saboda me? Saboda kawai suna da tabbacin cewa zafin dutse zai dumama cikin su da bayan su, har […]

Matan Sin na kwanciya a falalen dutsen don maganin cututtuka
Matan Sin na kwanciya a falalen dutsen don maganin cututtuka

Kafar sadarwa ta Hket.com ta ruwaito labarin yadda mata a yankin shaandi na kasar Sin ke kwanciya a falalen dutse don maganin cututttuka. Gungun matan wannan yanki kanj samu falalen dutsen da ya sha kunar rana. Ko saboda me? Saboda kawai suna da tabbacin cewa zafin dutse zai dumama cikin su da bayan su, har su samu waraka daga cututtuka.
Likitoci sun gargade su kan lallai su guji wannan tsohuwar al’ada., Domin a cdewar su babu inda kimiyya ta nuna cewa, wannan hanya ce ta samu wartaka daga cututtuka. Kuma sun yi nmuni da cewa, mutane na iya kona jikin su, har zafin ranar ya yi sanadin shanyewar gabban jiki.